1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta saki sojan Indiya da ta kama

Mouhamadou Awal Balarabe
March 1, 2019

Matukin jirgin saman Indiya Abhinandan Varthaman ya koma gida bayan da Firaministan Pakistan Imran Khan ya bada umurnin a sake shi, lamarin da zai kyautata danganta tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3ELBq
Pakistan Indien Konflikt l Festgenommener Indischer Pilot
Hoto: picture alliance/AP Photo/Pakistan Military

A wani yunkuri na yayyafa ruwan sanyi ga rikicin da ya taso tsakanin Pakistan da Indiya, gwamnatin Pakistan ta mika wa takwararta matukin jirgin saman nan da ta tsare bayan da jirginsa ya fada yankin Kashimir. Daruruwan mutane dauke da tutocin Indiya ne suka tarbi Laftanar Kanar Abhinandan Varthaman saboda suna daukanshi a matsayin wani gwarzo da ke kare muradun kasarsa. Sai dai ana bayyana sako shi da Firaministan Pakistani Imran Khan ya yi, a matsayin wata alamar son "zaman lafiya" bayan takun saka tsakanin kasarsa da Indiya a cikin 'yan kwanakin baya-bayannan.

A karon farko a cikin shekarun da suka gabata, jiragen yakin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna sun yi arangama, lamarin da ya haddasa damuwa a duniya saboda dukkaninsu biyu sun mallaki makamin nukiliya. Dama Pakistan ta bude wani bangare na sararin samaniyarta kwana guda bayan rufe shi bisa dalilai na rikici da ke ci gaba da gudana tsakaninta da makwabciyarta Indiya.