1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta saki wani jagoran Al-Qaida

September 21, 2013

Kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun tabbatar da sakin Mullah Abdul Ghani Baradar, wanda wasu majiyoyin ke cewar zai isa Saudiyya ko kuma Turkiya.

https://p.dw.com/p/19lXG
Former Taliban fighters stand with their weapons during a ceremony after joining Afghan government forces in Herat on August 7, 2013. About 100,000 foreign combat troops, 68,000 of them from the US, are due to exit by the end of 2014, and NATO formally transferred responsibility for nationwide security to Afghan forces a week ago. AFP PHOTO/ Aref Karimi (Photo credit should read Aref Karimi/AFP/Getty Images)
Hoto: Aref Karimi/AFP/Getty Images

Tun da farko Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta yi shelar sakin tsohon mataimakin ƙungiyar na Al-Qaida da ke Afghanisatan.

Wata sanarwar da ma'aikatar ta fidda ta ce gwamnatin Pakistan ɗin ta yanke hukuncin sakin Mullah Baradar ɗin ne domin tana ganin hakan zai taimaka wajen samun nasarar shirin sulhun da ake yi da 'yan kungiyar ta Al-Qaida a Afghanistan. Duba da matsayi da ya ke da shi da kuma irin kusancinsa da Mullah Muhammad Omar wanda 'yan ƙungiyar ke bai wa girma sosai. Gwamnatin Afganistan ta bakin wani kakakinta Aimal Faizi ta yi marhabin da sakin.

A baya dai Amurka ta yi ta matsin lamba ga gwamnatin ta Pakistan don ta saki Baradar ɗin wanda aka kame tun a cikin shekara ta 2010.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Abdourahamane Hassane