1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Biya zai sake yin takara

Mohammad Nasiru Awal
July 13, 2018

Shugaban kasar Kamaru mai shekaru 85 da haifuwa da ke zama daya daga cikin shugabannin Afirka mafi dadewa kan kujerar mulki, ya sanar a wanan Jumma'a cewa zai sake tsayawa takara a zaben Oktoban bana

https://p.dw.com/p/31Q6N
Kamerun Präsident Paul Biya Archivbild 30.01.2013
Hoto: Patrick Kovarik/AFP/Getty Images

Wannan sanarwar sake yin takaran shugaba Paul Biya, na ne zuwa daidai lokacin da zaman zullumi ke karuwa sakamakon rikici da 'yan aware na yankin musu amfani da harshen Ingilishi da kuma zargin da ake wa dukkan sassan da ke rikici da take hakkin dan Adam.

Shi dai shugaba Paul Biya mai shekaru 85, wanda tun a shekarar 1982 yake kan mulki, ya sanar a shafinsa na Twitter cewa a shirye yake ya amsa kiraye-kirayen 'yan kasar ta Kamaru, inda ya kara da cewa yana sane da kalubalen da za su fuskanta tare domin tabbatar da hadin kan kasar da kuma cigabanta. Saboda haka zana tsaya takara a zaben shugaban kasa da ke tafe.

Ra'ayoyi 'yan kasar sun banbanta dangane da sanarwar da Shugaba Biya ya bayar.

Maurice Alondo, shugaban wata kungiya mai goyon bayan jam’iyyar RDPC mai mulki, nuna goyon bayansa ya yi. Ya ce: "A halin yanzu za mu iya cewa shi ne wani mai dama-dama, domin duk wadanda suke son zama shugaban kasa a nan Kamaru ba mu ga wani mai kazar-kazar ba, don haka mu a ganinmu a yanzu babu wani da zai iya canjin shi."

Shi kuwa a nasa bangare Paul Guiffo ya nuna rashin jin dadinsa da wannan labari. Ya ce: "Kamata ya tafi ritaya domin ya samu ya huta, domin uba ne. Ya yi abubuwa da dama domin al’ummar kasar Kamaru. Amma a hakikanin gaskiya ina tsammanin a wannan karo kam ya kamata ya je ya huta ya bai wa wani ragama tafiyar da mulkin kasa."

Wahlen in Kamerun kamerunische Wahlbehörde Schild ELECAM
Hoto: DW

Kamaru na fama da tashe-tashen hankula na 'yan aware da ke son kafa kasar Ambazoniya a yankin da ke amfani da harshen Ingilishi bisa yadda suka ce an mayar da su saniyar ware a harkokin tafiyar da kasar.

Rundunar sojin kasar ta ce a ranar Alhamis daddare ma 'yan aware sun yi wa wata tawagar ministan tsaro Joseph Beti Assomo kwantan bauna lokacin wata ziyara a yakin Kudu maso Yammacin kasar, abin da ya sanadi na mutuwar 'yan aware 10 a wata musayar wuta ta tsawon mintuna 30. Da yawa daga cikin tawagar sun ji rauni, amma ministan ya tsallake rijiya da baya.   

Hakan na zuwa ne bayan da rundunar sojin ta musanta hannun sojojinta a wani faifayen bidiyo da ya nuna yadda aka rufe fuskokin wasu mata da yara aka kuma bindige su har lahira bisa zargin cewa wai 'yan kunar bakin wake ne na Boko Haram.

Sai dai kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce binciken da ta gudanar ya tattara shaidar cewa dakarun Kamaru a cikin faifayen bidiyon. Ilaria Allegrozzi, ita ce mai bincike a kungiyar ta Amnesty a yankin tafkin Chadi.

Ta ce: "Mun gano cewa sojojin Kamaru suka aikata ta'asar godiya ta tabbata da majiyoyinmu da ke kasa. Mun kadu da yadda rundunar sojin ta ce labarin na bogi ne. Domin mun gabatar da kwararan shaidu. Kiranmu a garesu shi ne su tabbatar binciken da suka alkawarta yi sun yi gaskiya da adalci ba da wani boye-boye ba."

Tun ba yau kungiyoyin kare hakkin dan Adam na zargin hukumomin Kamaru da wuce gona da iri a yakin da suke yi da 'yan Boko Haram.