1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Kagame ya samu sabon wa'adi na uku

Salissou Boukari
August 5, 2017

Sakamakon farko na zaben Ruwanda ya bai wa Shugaba Kagame nasara. Bisa ga alkaluman da ake da su a halin yanzu dai Kagame na da kashi 98.66 cikin 100 yayin da abokan hamayyarsa ke da kasa da kashi daya cikin 100.

https://p.dw.com/p/2hjb9
Ruanda Wahlen- amtierender Präsident Paul Kagame (RPF)
Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya samu wa'adi na uku.Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com/G. Dusabe

An bada sakamakon na farko ne dai bayan da aka kidaya kashi 80 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Abokan takarar na Kagame guda biyu kowa ya samu kasa da kashi daya cikin 100. Sakamakon na farko dai ya nunar cewa mai bi wa Shugaba Kagame wato Philippe Mpayimana ya samu kashi 0.72 yayin da shi kuma Frank Habineza ya samu kashi 0.45 na yawan kuri'un da aka kidaya. Paul Kagame ya kasance mataimakin shugaban kasa sannan ministan tsaron kasar ta Ruwanda kafin majalisar dokokin kasar ta zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2000 sai kuma a shekara ta 2003 da kuma 2010 ya sake cin zaben inda nan ma ya samu fiye da kashi 90 na kuri'un da aka kada. A yanzu kuma Kagame ya samu wani sabon wa'adin mulki na uku inda zai shafe wasu shekaru bakwai ya na mulkin kasar ta Ruwanda.