Peter Greste na Aljazira ya koma gida
February 5, 2015Talla
Peter Greste ɗan jaridar ɗan asalin Ostareliya ya koma gida bayan an sako shi daga ƙasar Masar, Peter Greste ya kwashe sama da shekara guda a tsare bayan ɗaure shi da aka yi da nufin ya kwashe shekaru bakwai a gidan kaso saboda tuhume-tuhume da ake masa da suka haɗa da tallafa wa 'yan ta'adda.
Greste ya dai sauka a ƙasar ta Ostareliya a yau Alhamis inda ya yi jawabi ga manema labarai da ke dakon saukarsa a birnin Brisbane. Cikin jawabansa dai ya bayyana fatansa na ganin an sako 'yan uwansa da suka haɗa da Mohammed "
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdourahamane Hassane