1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pompeo ya kara ba wa kawayen Amirka tabbaci

Mohammad Nasiru Awal ZMA
February 6, 2019

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya kara jaddada wa kawayen kasar cewa janye dakarun Amirkan daga Siriya ba shi ne karshen fadan da Amirka ke yi da ta'adda ba.

https://p.dw.com/p/3CsAm
USA | Mike Pompeo | Global Coalition to Defeat ISIS
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/A. Brandon

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya kara jaddada wa kawayen Amirka cewa janye dakarun Amirkan daga kasar Siriya ba shi ne karshen fadan da Amirka ke yi a yankin ba.

A lokacin da yake jawabi ga abokannin kawance su kimanin 79 da suka hallara a birnin Washington don tattauna mataki na gaba a rikicin kasar Siriya, Pompeo ya ce har yanzu kungiyar IS na zama babbar barazana. Ya yi kira ga kawayen Amirka da su mayar da himma a kokarin murkushe IS.

Pompeo ya ce an shiga sabon zamani na 'yan Jihadi dole ne kuwa a sake salon yakin da ake yi da su. Dole a sa himma wajen musayar bayanan sirri tsakanin kawayen, inda hukumomin kasa za su taka muhimmiyar rawa. Ya ce fadan da ake yi ba dole ne ya zama wanda sojoji ke wa jagora ba. Ya ce janyewar dakarun Amirka ba shi ne karshe fadan da Amirka ke yi da ta'addanci ba.