1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin: Gagarabadau a fagen siyasar Rasha

Mohammad Nasiru Awal
August 9, 2019

A shekaru 20 da ya fara rike madafun iko, kuri'ar jin ra'ayin jama'a sun nuna 'yan Rasha sun fi ganin laifin gwamnati maimakon shugaban kasar a dangane da matsalolin da suke fuskanta.

https://p.dw.com/p/3NfGs
Japan Osaka | G20 Gipfel | Wladimir Putin
Hoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/I. Pitalev

A ranar 9 ga watan Agustan shekarar 1999 Vladimir Putin fara fitowa fili a fagen siyasar Rasha, lokacin da ya zama firaminista. A lokacin Putin wanda daga bayan ya gaji Boris Yeltsin a matsayin shugaban kasa, ba a san shi ba sosai.

Yanzu da yake wa'adin mulkinsa na hudu, baya ga daya da yayi a matsayin firaminista, an dade ana masa kallon gagarabadau a fagen siyasar Rasha, musamman idan aka dubi sakamakon kuri'un jin ra'ayin jama'a. Sai dai abubuwa sun fara sauyawa. A karshen wa'adin shugabancinsa na biyu a 2008 sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a ya ba wa ofishin shugaban kasa maki 35 fiye da na gwamnati, amma yanzu gibi ya ragu zuwa maki 23 a binciken da cibiyar VTSIOM ta yi. Wani binciken da cibiyar ta gudanar ya nuna cewa yarda da ake wa Putin ta ragu zuwa kashi 30 cikin 100 wanda shine mafi karanci tun lokacin da aka fara irin wannan bincike a 2006.

Russland Boris Jelzin and Wladimir Putin 1999
Boris Jelzin da Vladimir PutinHoto: picture alliance/AP Images

Ana danganta farin jininsa da matakin da ya dauka na cusawa 'yan Rasha kishin kasa da nuna alfahari da zama 'yan kasar. Putin ya hau kan karagar mulki a karshen shekarun 1990 lokacin da Tarayyar Soviet ta ruguje abin da ya janyo tabarbarewar tattalin arziki da tsarin zamantakewa. Ga Lev Gudkov daraktan cibiyar Levada mai zaman kanta da ke binciken ra'ayin jama'a yace Putin ya samu nasara a fagen siyasar duniya. A cikin gida kuwa an fi ganin laifin gwamnati.

Sabuwar dokar fanshon a watan Oktoban 2018 dai ta gamu da zanga-zangar adawa. A 'yan watannin nan kuma al'umar kasar na nuna rashin jin dadinsu da magudin zabe a zabukan gwamnan yankin gabas mai nisa na kasar. Tabarbarewar tattalin arziki da cin hanci da zargin da ake wa shugabannin na yin sama da fadi da dukiyar kasa na daga cikin abubuwan da ke dakushe farin jinin Putin yanzu a cewar masanin kimiyyar siyasa Aleksei Kurtov.
"Muna ganin yadda farin jinin Putin ya fadi. Muna ganin yadda zanga-zangar adawa da gwamnatinsa ta zama ruwan dare a kasar, a da a wasu daidaikun wurare ake yi, kuma ba sa daukar hankalin kafafan yada labaru. Ana cikin zaman dar-dar ba wanda Putin ake dorawa laifin matsalolin tattalin arziki da Rasha ke fama da su."

Russland Moskau Protest Opposition Polizei
'Yan zanga zangar adawa a birnin MoscowHoto: picture-alliance/AP Photo/A. Zemlianichenko

Shi ma Valery Fyodorov na cibiyar jin ra'ayin jama'a ta VTSIOM ya ce duk da matsin tattalin arziki da batun kiwon lafiya da kuma bukatar karin albashi, Putin na da goyon bayan daukacin 'yan kasar.


"Al'umma na gode wa Putin, suna girmama shi sun kuma dora fatansu a kanshi. A nan ina magana ne a kan akasarin 'yan kasar, amma ba wai dukka 'yan kasa ba. Akwai wadanda ba su gamsu da mulkinsa ba, suna kuma neman sauyi. Sai dai ba su da yawa."

Masanin ya ce manufofin siyasar Putin sun dauki sabon salo na sauyin alkiblar tattalin arziki da zamantakewa inda ya yi alkawarin inganta matsayin rayuwar al'umma ya kuma farfado da tattalin arzikin Rasha.))