1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyin da jaridun Jamus suka buga kan nahiyar Afirka a wannan makon.

YAHAYA AHMEDNovember 4, 2005

A wannan makon ma, jaridun Jamus da yawa sun waiwayi nahiyarmu ta Afirka, inda suka rubuta sharhohi da dama kan al’amuran da ke wakana a sassa daban-daban na nahiyar. Sai dai, a galibi, duk makalan da aka rubuta, sun shafi yankuna ne da ake ta fama da matsaloli ko kuma rikice-rikice. Da wuya dai a sami wata jarida a kasashen yamma, da ke buga labarin wani abin alfahari game da nahiyar ta Afirka.

https://p.dw.com/p/BvQG
`Yan zanga-zanga a birnin Abidjan na kasar Côte d'Ivoire.
`Yan zanga-zanga a birnin Abidjan na kasar Côte d'Ivoire.Hoto: AP

Sharhohin wannan makon da galibin jaridun Jamus suka buga a kan nahiyar ta bakar fata, sun shafi rikice-rikicen da ake yi ne a kasashen Côte d’Ivoire, da Habasha, da Eritrea da kuma matsalar karancin ruwa da gurbacewar yanayi a nahiyar.

To za mu fara ne da kasar Côte d’Ivoire, inda a karshen makon da ya gabata ne wa’adin shugaban kasar Laurent Gbagbo ya cika, amma saboda zarcewar da ya yi kan mulki, aka yi wata mummunar zanga-zanga a birnin Abidjan da wasu manyan biranen kasar. A kan halin da ake ciki a Côte d’Ivoire din ne, jaridar die tageszeitung ta yi sharhinta.

„Rikice-rikicen kasar Côte d’Ivoire, sun hana daukan matakan yanke shawara kan kafa sabuwar gwamnati a kasar“, inji jaridar. Bisa kuduri mai lamba 1633 ta Majalisar dinkin Duniya dai, da ya kamata a ce tun farkon wannan makon, kasar na da sabon Firamiya, mai cikakken iko, a gefen shugaba Laurent Gbagbo, wanda aka amince ya ci gaba da rike mukaminsa bayan cikar wa’adinsa, har zuwa wani takaitaccen lokaci. Amma bisa dukkan alamu, ba za a tinkari nada sabon Firamiyan ba sai bayan ziyarar da masu shiga tsakani, wato shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da na Afirka Ta Kudu, Thabo Mbeki, za su kai a kasar. Kafin wannan lokacin dai, Laurent Gbagbon ne zai ci gaba da jan ragamar mulki a kasar.

Jaridar ta kara da cewa, ba samun wanda zai rike mukamin Firamiyan ne ke da wuya ba. Amma dagewar da Najeriya da Afirka Ta Kudu suka yi, kan cewar su ne za su nada wanda zai fi dacewa da mukamin, ita ce babbar matsalar da ke hana ruwa gudu. Saboda kasashen biyu na barazanar sanya wa duk wanda bai amince da zabinsu ba takunkumi.

daya matsalar kuma, ita ce halin ake ciki a fagen siyasar kasar, inda abokan hamayya na bangarorin biyu, wato na gwamnati da na `yan tawaye bas a ga maciji da juna. An dai jiyo daga bakin shugaba Gbagbo a cikin `yan kwanakin da suka gabata, yana mai cewar, babu wata yarjejeniya ko kuma wani kudurin Majalisar dinkin Duniya, wadanda suka isa su janye kundin tsarin mulkin kasar, ko kuma su hana shi aiki. A cikin kundin dai, shugaban kasar, shi ya fi rinjayin madafan iko da Firamiya. To amma, tuni, `yan tawayen Côte d’Ivoire din, wadanda ke rike da duk yankunan arewaci ko kuma rabin kasar gaba daya, sun gabatad da shugabansu Guillaume Soro, tamkar sabon Firamiyan. A halin da ake ciki kuma, ban da tsohon shugaban kasar, Henri Konan Bédié, duk jam’iyyun adawan kasar suna nuna goyon baya ga shawarar nada shi Soro din a mukamin Firamiya.

Jaridar die tageszeitung, ta kammala dogon sharhinta ne da aran bakin wani dan jaridar kasar, Moussa Touré, yana mai cewar talakawan kasar dai sun kosa da irin halin da ake ciki, wanda ya ki ci ya ki cinyewa. Da yawa daga cikinsu ma na kira ne ga juyin mulki irin na soji. Idan ko gamayyar kasa da kasa ba yi katsalandan a cikin wannan batun ta kuma kwance wa mayakan bangarorin biyu damara ba, to babu shakka abin da zai auku ke nan a kasar ta Côte d’Ivoire.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi sharhinta ne kan damuwar da Majalisar dinkin Duniya ke nunawa game da barazanar barkewar wani sabon yaki tsakanin kasashen Eritrea da Habasha. A ran larabar da ta wuce ne, inji jaridar, babban Sakataren Majalisar, Kofi Annan, ya bayyana bacin ransa ga rahotannin da ke nuna cewa, ana ta lura da karin yawan kai kawon rukunan sojoji a arewaci da kuma kudancin layin nan da aka shata tsakanin-kasashen biyu, a karshen yakin da suka gwabza da juna a cikin shekara ta 2000. Bisa wani rahoton da ofishin manzancin Majalisar dinkin Duniya a kasashen biyu ya buga dai, tuni an tara bataliyoyin dakaru da na sojojin kundumbala daga bangarorin biyu a kan iyakar, dukkaninsu da shirin ko ta kwana. Tuni dai inji jaridar, Kofi Annan, ya yi kira ga bangarorin biyu da su yi taka tsantsan, kada kuma su dau wasu matakan da ko wane bangare zai ga kamar tsokanarsa dayan ke yi, har ya kai ga musayar wuta da kuma tabarbarewar al’amura tsakaninsu.

Jariadar Berliner Zeitung ta yi sharhi ne kan wani taron kasa da kasa da aka bude a birnin Nairobin kasar Kenya, don tattauna batun tauyewar da wasu manyan tafkunan Afirka ke yi a halin yanzu. Wani binciken da aka gudanar, da kuma hotunan tauraron dan Adam ko kuma satellite a turance, da aka dauka na nuna cewa gurbacewar yanayi na ta kara habaka a nahiyar Afirka, abinda kuma ke ta kara janyo kankancin tafkunan da ake samu. Alal misali, inji jaridar, hotunnan na nuna yadda tafkin Songor da ke kasar Ghana, ya kusan shanyewa ma gaba daya, ko kuma tafkin Cadi, wanda ya huskanci tauyewar kashi 90 cikin dari a shekaru 10an da suka wuce. Kazalika kuma, kogin nan na Zambeszi a kudancin Afika, na huskantar bushewa, saboda madatsar ruwan Kabora-Bassa da kasar Mozambique ta gina.