1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Raguwar aiwatar da hukuncin kisa a duniya

April 10, 2013

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa Amnesty International ta wallafa rahoto na shekara ta 2012 wanda ya nuna cewa an rage aiwatar da hukunci kisa a duniya.

https://p.dw.com/p/18DNl
Hoto: picture-alliance/dpa

Rahoton na kungiyar ta Amnesty International ya nuna raguwar kasashen duniya masu aiwatar da hukuncin kisa. Amma a daya hanun kuma an samu karuwar mutanen da a ka zartas musu da hukucin da mutane biyu idan aka kwatanta da shekara ta 2011. Rahoton ya tabbatar da cewa akalla mutane 682 aka zartas musu da hukuncin. Sai dai wadannan alkaluma babu na kasar China a ciki, saboda kasar ke kan gaba, kuma alkaluman kasar kan zama cikin sirri.

Kungiyar ta nunar da cewa an yanke hukuncin kisa kan mutane 1,722 cikin kasashe 58, wanda ke nuna raguwa bisa shekara ta 2011, na mutane 1,923 cikin kasashen duniya 63. Kasashe 21 na duniya ke ci gaba da zartas da hukuncin.

Amnesty International Logo
Kungiyar Amnesty ta yi kira da aka dakatar da hukuncin kisaHoto: picture-alliance/dpa

Matsayin Afirka game da hukuncin kisa

Amnesty International ta ce kasashen Afirka na cikin wuraren da ake samun raguwar zartas da hukuncin kisa. Kamar yadda mai baiwa kungiyar shawara kan yanke hukunci kisa Jan Wetzel ke cewa:

''A gaskiya ba kasafai ake zartas da hukuncin kisa a Afirka ba. A cikin shekara ta 2012, an zartas da hukuncin cikin kasashen nahiyar biyar, wanda ya saba da yadda ake gani a kasashen cikin shekarun baya na samun kasashe biyu zuwa hudu na Afirka. Amma wannan karon bayan kasashen Gambiya da Botswana sun dawo da aiwatar da hukuncin kisan, an samu rahoton karuwar aiwatar da hukuncin a Sudan.''

A cikin rahoton, Amnesty ta kara da cewa, kasar China ke kan gaba cikin kasashen da ke aiwatar da hukuncin kisa, kuma an zartas da hukuncin na kisa fiye da sauran kasashen idan aka hada baki daya. Kasashen Iran, Iraki, Saudiya, da Amirka ke mara baya ga China.Rahoto ya nuna takaici da dawowa da aiwatar da hukuncin kisa a kasashen Indiya, Japan da Pakistan, wanda ya ce, hakan koma baya ne.

Kungiyar ta Amnesty ta nuna matukar damuwa da yadda kasar Iraki ta zartas da hukuncin kisa kan mutane 129 cikin shekara ta 2012, wanda ke nuni da nunkin na shekara ta 2011. Jan Wetzel ya yi bayani bisa dalilan kungiyar na adawa da hukunci kisa ta ko wani hali:

Infografik Vollstreckte Todesstrafen 2012 Chinesisch
China ba ta bayyana yawan mutanen da aka kashe.

''Amnesty International ta na adawa da hukuncin kisa ta ko wani hali, ko mutumin ya aikata laifi ko bai aikata ba, da menene ya faru.''

Cikin kasashen Asiya, Indiya wadda tun shekara ta 2004, ta yi watsi da zartas da hukuncin na kisa, ta aiwatar da hukuncin cikin shekarar da ta gabata ta 2012, kan Ajmal Kassab dan bindiga dadi, dan kasar Pakistan, wanda a ka samu da hanu wajen tayar da bam, a wani Otel da ke birnin Mumbai cikin shekara ta 2008. Yayin da Pakistan ta aiwatar a karon farko tun cikin shekara ta 2008.

Kungiyar ta ce akwai nasarori cikin kasashen duniya bisa yadda kasashe masu yawa babu aiwatar da hukuncin na kisa. Rahoton ya gano nasara kan matakin kawar da hukuncin kisa tsakanin yankunan duniya baki daya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe