1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan Transparency na 2012 akan cin hanci

December 5, 2012

Ƙungiyar yaƙi da cin hanci da rashewa ta kasa da kasa ta bayyana Najeriya a matsayi na 139 da Nijar 113 a jerin ƙasashen duniya da ke fama matsalar cin hanci da Rashawa.

https://p.dw.com/p/16wKb
***Das Logo darf nur in Zusammenhang mit einer Berichterstattung über die Institution verwendet werden *** Transparency International, kurz TI, ist eine weltweit agierende nichtstaatliche Organisation mit Sitz in Berlin, die sich in der nationalen und internationalen volks- und betriebswirtschaftlichen Korruptionsbekämpfung engagiert. Quelle;: Wikipedia
Transparency International Logo

Batun Cin hanci da rashawa, abu ne da akan ce ya zama ruwan dare gama duniya . Duk da cewa hukumomi masu fafatakar kare hakin Bil -adama sun tashe haikan ga yaƙar wannan al-amari a duk kasashen duniya, inda har ma ya kai ga hamɓarar da wasu shuwagabanin ƙasashen da aka same su da laifufuka da ke da nasaba da cin hanci da rashawa .

Wanan shekara kuwa, ga dai bayyanin da ƙungiyar yaki da cin hanci da rashawa,har ila yau haƙar wasu ƙasashen bata cimma ruwa ba tukun, domin kashi biyu daga cikin uku na kasashe 176 da akayi nazarinsu, shuwagabani na amfani da mukaman su ta hanyar da bata dace ba, tare da yin almundahana da dukiyar talakawansu.

Ƙasashen Afganistan, koriya ta arewa da Somaliya, sune ke a sahum gaba a matsayin waɗanda cin hanci da Rashawa ya yi musu katutu, a yayin da kuma ƙasashe kamar su Denmark, Finland da New Zealand suka zo karshe a matsayin waɗanda matsalar su bata taka kara ta karya ba.

Srirak Plipat
Srirak PlipatHoto: Transparency International

Edda Müller mai bada shawarwari ce kan yaki da cin hanci wadda ta danganta wannan matsalar da matsayin tattali. "Akasarin matsaloli na cin hanci da ake fuskanta a yawancin kasashe suna da alaka ne da matsayin tattalin arzikin waɗannan kasashen, wadanda ake gani a zahiri".

A nahiyarmu ta Afrika kuwa Najeriyace ta kasance a matsayi na 139, janhuriyar Nijar 113, kana Ghana ta zo na 64. Wannan na nuni da cewar har yanzu da sauran tafiya a fafutukar da ake yi na yakar cin hanci.

Afganistan kasa ce da har yanzu ke fuskantar matsalolin na tashe tashen hankula, amma duk da haka ta kasance cikin jerin kasashen da cin hanci ke cigaba da zama kadangaren bakin tulu. Sriraka Plipat shine Shugaban ƙungiyar Transperancy International mai kula da yankin Asia.

Ina ganin wannan alama ce dake nuna cewa ƙasar na cikin baban matsala na cin hanci,matakai na kiyaye hakan duk sun yi rauni . Ana kuma batun baban bakin kasar faa ake ke, gimshikin tattalin arzikin kasar.

Halin da Afganistan ta tsinci kanta a ciki, kara razanar da mutane yake, bisa la-akari da cewa kasar ko da ma na fama da matsaloli tsaro da kuma sukurkucewar tattalin arziki kuma ga abinda shuwaganabi su sa a gaba?

Paulo Morais
Paulo MoraisHoto: TIAC

Srirak plipat ya kara da cewa "kuɗaɗen da yakamata inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya duk an rasa inda suka shiga.A sakamakon hakan duk wasu abubuwa da cigaban ra-uwa kara tabarbarewa suke.Kashe goma daga cikin kasafin kuɗin ƙasar an rasa inda suka bi wannan baban matsala ce ga al-umar ƙasa."

Sai dai kuma shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa Cobus da Swardt ya Jaddada kira da ga shuwabananin kasashe masu karfin tattalin arziki da su zage damtse wujen yaki da cin hanci , domin kasancewa abin koyi ga kasashe masu tasowa .

To in har kuwa basu sake sheka ba a cikin gida , hakan zai kara 'ya ya tawa ne zuwa kasashen duniya tun da kasashen da damma na koye da su.

Mawallafiya: Maryam Mohammed Sissy
Edita : Zainab Mohammed Abubakar