1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Amnesty a kan hukuncin kisa

April 10, 2013

Kungiyar kare hakin Bil Adama ta kasa da kasa, ta Amnesty International, ta wallafa wani rahotonta a dangane da hukuncin kisan da ake zartarwa a duniya.

https://p.dw.com/p/18Coq
Amnesty International

Daga cikin kasashen da kungiyar Amnesty International dake kula da kare hakkin Bil Adama ta nuna da yatsa gurin zartar da hukuncin kisa a duniya, sun hada da Saudiya, Iran, Amirka, Iraki, China, Yemen, Japan da kuma Indiya.
A cikin wani rahotonta na bana da kungiyar ta wallafa, kimanin mutane 682 ne aka zartaswa hukuncin kisa a cikin kasashe 21 na duniya.
Yanzu haka mutane 7 ne aka rataye a kasar Iraki a cikin makon nan a daidai lokacin da kungiyar ke zaman taronta. To sai dai duk da hakan kungiyar tace an samu sauki, a la'akari da hukunce hukuncen kisan da aka zartar a shekara ta 2011 inda mutane 1.923 aka yankewa wannan hukuncin daga cikin kasashe 63. Kungiyar ta kuma nuna bacin ranta ga abunda ta kira koma bayan kasar Japan wadda ita ma yanzu ta sake shiga sahun kasashen dake zartar da makamancin wannan hukuncin bayan da kasar ta share watani 20 ba tare da an yankewa kowa hukuncin kisa ba .

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu