1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rana ta biyu ga shari´ar Saddam Hussain a Bagadaza

March 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6M

An koma ci gaba da sauraron shari´ar tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussain da mukaraban sa guda bakwai a can birnin Bagadaza.

Wannan dai shine karo na biyu a zaman wannan kotu , a tun bayan da kotun ta dage sauraron karar na tsawon makonni biyu da suka gabata.

Tuni dai masu gabatar da kara suka gabatar da bayanan dake nuni cewa akwai sa hannun Saddam Hussain , a cikin kisan kiyashin daya auku akan mutane 148 yan shi´a a garin Dujail a shekara ta 1982.

Jim kadan da zaman kotun a yau kuma, shugaban masu gabatar da karar, wato Jaafar Al Mussawi ya gabatar da wata takarda dake dauke da sa hannun Saddam , wacce a cikin ta tsohon shugaban kasar ya yafewa biyu daga cikin mutanen daya bayar da umarni a kashe su.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa wannan zama na gudana ne a cikin dar dar na sake barkewar rikici na kabilanci, wanda a yan kwanakin nan yayi ajalin mutane sama da dari.