1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yaki da zazzabin cizon sauro

April 25, 2013

Kamar a ko wace shekara, a bana ma, Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 25 ga watan Aprilu a matsayin ranar yaki da cutar Malaria, da ta zama gagara-badau a kasashe matasa

https://p.dw.com/p/18NKk
Hoto: picture-alliance/dpa/ Birgit Betzelt/actionmedeor

Sakamakon karuwar yawan mace macen mutane daga cutar zazzabin cizon sauro musamman a Afirka, ya sanya a yanzu haka aka kirkiro da wani gidan sauro da za'a iya amfani da shi na lokaci mai tsawo, ba tare da maganin da aka sanya masa ya kare aiki ba, kamar na wadanda ake da su.

Binciken da hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dunkin Duniya ta gudanar na nuni da cewar, a ko wace shekara akalla mutane miliyan guda ne ke rasa rayukansu a fadin duniya daga cutar zazzabin cizon sauro watau malariya, kuma kashi 90 daga cikin 100 na mace macen a nahiyar Afrika ne. Shekaru masu yawa da suka gabata dai an kirkiro gidajen sauro masu yawan gaske wanda aka rigaya ka sanya musu maguguna, kuma za'a iya daura su a gadajen da ake amfani da su.

Wadannan gidajen sauro dai sun taimaka matuka gaya wajen kare mutane daga kamuwa da cutar ta malariya data kasance gagarabadau musamman a kasashen Afrika dake yankin kudu da sahara. Sai dai fa bayan wani lokaci akan samu raguwar karfin magungunan dake jikin gidan sauron, ma'ana tasirunsu zai ragu, musamman ma idan ana barinshi da kazanta ba tare da ana wankeshi ba.

Akasarin wadanda ke mutuwa daga cutar ta zazzabin cizon sauro dai, yara ne kanana, wadanda shekarunsu basu shige biyar da haihuwa ba. Hakan kuma yana nasaba ne da cewar, yaran suna kwanciya da wuri fiye da manya, a wannan lokacin ne kuma sauron dake yada cutar ta malaria keda kuzarin cizo. Adangane da haka ne gidan sauron yake da matukar muhimmaci a cewar likita Jürgen May, dake cibiyar nazarin cututtukan magungunan cututtuka da suke da gandun dasuka da yawaitar ruwan sama na Bernhard-Nocht...

Moskitonetz
Gidan sauro-maganin cutar MalariaHoto: Edlena Barros

Ya ce " har ya zuwa yau wannan iatace hanya mafi muhimmanci na samun kariya daga cizon sauron dake yada cutar malaria, wadanda kuma da dare ne suke da kuzarin yada cutar".

Daura gidan sauro a jikin gado yana da matukar muhimanci a kula dashi a kullum, kamar yadda mutum zai goge hakoransa kullum. Domin da zarar mutum yayi ganganci, ko shakka babu sauro zasu sheke ayarsu. Dr May ya ce

"Ko shakka babu mutane zasu ci moriyar wannan gidan sauro, idan har anyi amafani dashi kamar yadda aka tsara da magungunan dake cikinsa, tare da tabbatar da cewar babu rami ko huji a jikinsa. Zai dauki lokaci mai tsawo ana amfani dashi".

Abun da ke da muhimmanci dangane da gidan sauron da ake dashi dai shine, sai an rika fesa masa magani musamman, bayan wanda aka yi shi dashi ya kare, bisa wankewa ko kuma jimawa ana amfani dashi. Dalili kenan daya sa aka kirkiro wannan sabon gidan sauro wanda yafi na da din tasiri, acewar Fredric Baur. A matsayin shi na masanin kimiyyar harkokin noma a cibiyar kimiyyar shuke shuke ta Bayer dake Lyon, dake nazarin kan cututtukan da kwari ke yadawa. Yace:

Malaria Sudan Kind
Cutar Malaria tafi illa ga yara kananaHoto: Getty Images

"Ana sanya maganin ne sannu a hankali tun lokacin sarrafa shi gidan sauron, maganin yana fitowa daga jikinsa sannu a hankali, koda kuwa bayan an wanke shi ne, kuma zaka iya wanke shi sau 30, amma maganin yana jikinsa kamar yadda kungiyar kula da lafiya ta MDD ta tabbatar".

Wannan sabon gidan sauro dake dauke da maganin kare mutum daga cizon sauro dai baya wari. Kuma kamfanin Bayer dake sarrafa shi yayi alkawarin samarda miliyoyin sabbin gidajen sauron da ake kira life-Net, musamman domin kare yara wadanda sune suka fi mutuwa daga cutar ta zazzabin cizon sauro.A fadin duniya baki daya dai, Mutane tsakanin miliyan 300 zuwa miliyan 500 ke fama da cututtukar da ake kamuwa dasu.

Mawallafiya:Zainab Mohammed
Edita: Umaru Aliyu