1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsar da shugabar Afrika ta Tsakiya

January 23, 2014

Catherine Samba-Panza za ta kasance mace ta farko da aka nada shugabar gwamnatin rikon kwarya a Janhuriyar Afrika ta Tsakiya da rikicin siyasa da na addini ya mamaye.

https://p.dw.com/p/1Aw6J
Catherine Samba-Panza Zentralafrikanische Republik 20.01.2014 Bangui
Hoto: Reuters

A yau ne ake rantsar da Catherine Samba-Panza a matsayin shugabar gwamnatin rikon kwarya a janhuriyar Afrika ta tsakiya. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar kasar ke cikin yanayi na fargaba dangane tashe tashen hankulan dake da nasaba da addini da ya mamaye kasar. Zaben Samba-Panza a makon da ya gabata dai, na bangaren sake kaddamar da tsarin siyasa a wannan kasa da rigingimu ya mamaye, bayan yin murabus din shugabannin mulkinta. Ana fatan cewar zaben Samba-Panza zai taimaka wajen samar da zaman lafiya, kasancewarta Christa, wadda kuma bangarorin biyu masu fada da junan ke daraja wa.

A ranar 20 ga watan janairu ne dai majalisar dokoki na rikon Afrika ta tsakiyar, ta zabi Samba-Panza a matsayin shugaban kasar ta farko, a jerin sunayen 'yan takara guda takwas da aka gabatar, ciki har da tsohon shugaban gweamnatin rikon kwarya Michel Djotodia da fraiministan riko Nicolas Tiangaye.Kimanin mutane miliyan 2.2 dake zama rabin al'ummar kasar ne dai, ke bukatar agajin gaggawa a cewar MDD.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal