1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasa rayuka saboda Ebola zai ninka sau uku cikin makonni

September 23, 2014

Duk da kokarin kasashen duniya da suka bayyana aniyar yaki da cutar Ebola, binciken masana na nuna cewa se an yi da gaske kan wannan cuta me aniyar kare dangi.

https://p.dw.com/p/1DJ97
Ebola Tote in Liberia
Hoto: Dw/J. Kanubah

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa adadin mutanen da suke kamuwa da cutar Ebola za su kai 20,000 nan da watan Nuwamba idan har ba a dauki wani babban mataki ba.

Christopher Dye shugaban sashin da ke lura da tsare-tsare a hukumar wanda kuma ya jagoranci wannan bincike, ya ce idan har ba a tsaida wannan annoba ba cikin gaggawa tana iya zama bala'i mai muni.

Ya ce idan baa yi da gaske ba kan yaki da wannan annoba na iya daukar shekaru musamman ma a kasashen na yammacin Afrika inda tuni ta halaka mutane 2,800.

Cikin wannan bincike an gano cewa idan babu ingantattun matakan dakile wannan cuta ta Ebola, mutanen da suke rasa rayukan su ta sanadin kwayoyin cutar ta Ebola zasu cigaba da karuwa daga daruruwa da suke mutuwa cikin mako zuwa dubbai cikin mako guda.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu