1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadin kai zai taimaka wajen yaki da ta'addanci

Abdullahi Tanko Bala
November 2, 2017

Shugabanin kasashen Rasha da Iran da Azerbaijan sun tattauna kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki da samar da tsaro a yankin da ma samar da mafita a rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/2mu1a
Iran Wladimir Putin & Hassan Rohani in Teheran
Hoto: picture-alliance/dpa/TASS/M. Metze

Shugabanin kasashen Rasha da Iran da Azerbaijan sun tattauna kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki da samar da tsaro a yankin da ma samar da mafita a rikicin Siriya.

Bayan zama da shugabanin uku suka yi sun kuma yi jawabi ga manema labarai a birnin Tehran, shugabannin Hassan Rouhani na Iran mai masaukin baki da Vladimir Putin  na Rasha da Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev sun baiyana cewa hadin kan da aka samu tsakanin kasashen uku ya taimaka wajen yaki da ta'addanci a yankin.

Syrien Astana - Friedensgespräche
Hoto: Getty Images/AFP/S. Filippov

A jawabinsa shugaban Iran hassan Rouhani ya ce sun tattauna dangantaka tsakanin kasashen uku da rawar da suke takawa ta fuskar tsaro, Iran da Rasha na aiki wajen yaki da 'yan ta'adda da kokarin samar da zaman lafiya a Siriya. Ya kara da cewa suna aiki da Rasha da Turkiya wajen ganin tattaunawar Astana ta dore. 

A nasa bangaren shugaba Putin ya ce babu wata kasa daya tilo da za ta iya tunkarar matsaloli irin na Siriya don samun mafita face ta nemi abokan hadin gwiwa.

Russland Putin trifft Menschenrechts-Rat
Hoto: picture alliance/Russian Look/Kremlin Pool

Iran da Rasha dai na zama manyan kawaye ga Shugaba Bashar al-Assad yayin da Amirka da Turkiya da sauran kasashen Larabawa ke mara baya ga 'yan tawaye da ke kokarin ganin bayansa. Sai dai dukkanin kasashen na da abokin gaba guda wato kungiyar IS. 

Da ya koma ta fuskar tattalin arziki shugaba Putin ya ce Rasha da Iran da Azerbaijan manya ne kan albarkatun mai da ake hakowa duk da cewa ba suna gasa ba ne, amma suna hada kai cikin kungiyar kasashe da ke fitar da albarkatun man fetir (OPEC) da kuma kasashen da ba mambobi ba.