1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Rasha da Turkiyya za su gana

Zulaiha Abubakar
December 29, 2018

Rahotanni daga Moscow sun bayyana cewa ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Turkiyya za su gudanar da wani taro domin tattauna matakin da gwamnatin Amirka ta dauka na janye sojojin kasarta daga Siriya.

https://p.dw.com/p/3AlP8
Litauen Exercise Baltic Operations | US-Soldaten bei Landung
Amirka na son janye sojojinta daga kasashen Siriya da AfghanistanHoto: Getty Images/AFP/P. Malukas

Shugaban kasar Amirka Donald Trump dai ya bayyana shirin kasarsa na janye sojojinta da ke kasar Siriya da yawansu ya kai 2000, da nufin kawo karshen tsare-tsaren Amirka a yankin Gabas ta Tsakiya. A wani sabon labarin kuma, Amirkan na sake duba batun janye sojojinta da ke aikin yaki da ta'addanci a kasar Afghanistan wadanda yawansu ya kai 7000, duk kuwa da cewar 'yan ta'adda na ci gaba da kai farmaki a wasu yankuna na kasar ta Afghanistan.