1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala zaben majalisar dokokin Rasha

Ramatu Garba Baba
September 20, 2021

Jam'iyyar United Russia Party da ke goyon bayan Shugaban Rasha Vladimir Putin ta sami nasara lashe akasarin kujerun majalisar dokoki a zaben da aka kammalla a karshen mako.

https://p.dw.com/p/40XvB
Russland Parlamentswahlen Auszählung
Hoto: Evgenia Novozhenina/REUTERS

Sakamako na zaben 'yan majalisar dokokin Rasha da aka kamalla gudanarwa a karshen makon da ya gabata, ya nuna cewa jam'iyyar United Russia Party da ke goyon bayan Shugaba Vladimir Putin ta sami nasara lashe akasarin kujerun majalisar, da akalla kashi 64 cikin dari na kuri'un da aka kada. Duk da wannan rinjaye, ana ganin jam'iyyar ta rasa tagwamashi idan aka kwatanta da sauran zabukan da suka gabata.

Zaben na Rasha ya gudana duk da kokawar jama'a kan matsa wa masu sukar lamirin shugaban kasar lamba, inda kafin soma zaben, aka kama tare da tsare dandazon masu goyon bayan madugun adawar kasar Alexie Navalny, wanda shi ma ke tsare tun cikin watan Janairun bana.