1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kakaba wa Amirkawa 29 takunkumi

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
April 21, 2022

A karon farko Rasha ta bayyana sunayen shugaban kamfanin Meta ko Facebook Mark Zuckerberg da mataimakiyar shugabar kasar Kamala Harris a cikin jerin mutane Amirkawa 29 da ke fuskantar takunkumi.

https://p.dw.com/p/4AG7O
USA | Zuckerberg spricht in der Georgetown University
Hoto: picture-alliance/dpa/Bildfunk/AP/N. Wass

Rasha ta haramta wa Amirkawa 29 shiga kasarta ciki har da shugaban kamfanin Meta ko facebook  Mark Zuckerberg da mataimakiyar shugabar kasar Kamala Harris, a wani matsayi na martani kan jerin takunkuman da Amirka ta kakaba mata tun bayan da ta soma gwabza yaki da makwabciyarta Ukraine.

Ko baya ga 'yan kasar ta Amirka Moscow ta kuma kakaba wa 'yan Canada 61 galibi kusoshin gwamnatin kasar takunkumin shiga kasarta, duk a wani mataki na rama wa kura anniyarta.

Sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce 'yan kasashen biyu da takunkumin ya sahafa, ba za su sake saka kafa a cikin kasarta ba har sai abinda hali ya yi.

A baya dai Rasha ta kakaba takunkumi ga jagoraorin kasashen ciki har da shugaba Biden na Amirka da firaministan Canada Justin Trudeau a matsayin martani ga jerin takunkumai da aka aza mata