1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta janye daga wakilci a NATO

Suleiman Babayo ATB
October 18, 2021

Mahukuntan Rasha sun dauki matakan katse hulda da kungiyar tsaron NATO/OTAN bisa martani cewa Rasha ta tura 'yan leken asiri wakilci helkwatar kungiyar.

https://p.dw.com/p/41piK
Russland PK Sergei Lawrow und Josep Borrell
Hoto: Russian Foreign Ministry/REUTERS

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kasarsa za ta dakatar da aiki na wakilci a kungiyar tsaro ta NATO/OTAN da ke birnin Brussels na kasar Beljiyam daga farkon wata mai zuwa na Nuwamba sakamakon kwace takardun aiki na jami'an diflomasiyar kasar. Bugu da kari, Rasha za ta rufe ofishin NATo da ke birnin Moscow fadar gwamnatin kasar.

Sergei Lavrov ministan harkokin wajen na Rasha ya fadi haka yayin taron manema labarai, inda ya ce haka na zama martani kan karbe takardun aikin jami'an diflomasiyan Rasha guda takwas daga kungiyar tsaron ta NATO bisa zarge cewa 'yan leken asiri ne da ake rufa-rufa.

Sai dai a cikin martani Heiko Maas ministan harkokin wajen Jamus ya bayyana matakin na Rasha a matsayin abin takaici. Maas ya shaida wa manema labarai a Luxembourg cewa kasashen kungiyar tsaron ta NATO suna shirye da tattaunawa da mahukuntan Rasha maimakon fito na fito.