1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta zargi Jamus da bata mata suna

April 4, 2014

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta mika korafinta ga jakadan kasar Jamus a Rashan kan abun da ta kira da bata suna da ministan kudi na Jamus din yai mata.

https://p.dw.com/p/1Bbku
Hoto: picture alliance / AP Photo

Ministan kudin na Jamus Wolfgang Schäuble dai ya bayyana mamayar da Rashan ta yi wa yankin Kirimiya na Ukraine a matsayin irin ayyukan da Adolf Hitler ya yi gabanin yakin duniya na biyu a yayin da yake jawabi ga wasu yara 'yan makaranta. Ita ma dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana matakin Rashan a yankin Kirimiya da wani abu da ya sabawa dokokin kasa da kasa. A hannu guda kuma ministocin harkokin kasashen ketare na kungiyar EU za su fara wani taro na yini biyu inda ake sa ran batun yankin Kirimiya ne zai mamaye tattaunawar tasu. Taron nasu dai na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban Amirka Barack Obama ya sanya hannu kan amincewa da baiwa Ukraine bashin dalar Amirka biliyan daya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar