Rashin kula da talakawa shine matsalar Najeriya
November 14, 2012Gwamna Kashim Shetima na jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya mai fama da tashin hankalin da ake dangantawa da Boko Haram ya yi gargadin cewa matukar gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya ba su yi adalci wa talakawan su gami da jan su a jiki ba, to kuwa mulki yankunan su zai iya gagarar su nan gaba.
Gwamnan wanda yake bayanin kan hanoyin da za'a magance matsalar Boko Haram, yace tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a yankunan Arewacin Najeriya suna da nasaba da yadda shugabannin yankin suka yi watsi da talakawan su, inda suka bige da tara kudade don gudun talauci.
Yace kamata ya yi gwamnonin da sauran wadanda aka zaba su cika alkawuran da su ka yi wa talakawa maimakon nuna mulki ko karfin iko ko kuma sama da fadi tare da barin talakawan cikin kangin talauci da rashin aiki. Wannan a cewar sa ba zai haifar da alheri ba kuma masu mulkin za su iya rasa shi anan gaba, ganin talakawa sun fara gane abinda duniya ke ciki.
Masu fashin baki da talakawan kasar sun gaskata wannan furuci na gwamnan inda suka bukaci masu fada aji a yankin su rungumi talakawa ba tare da nuna kyama ba, in suna so su tsira da mutunci a idon talakawan. Dr Sadiq Umar Abubakar wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum ya gaskata wannan gargadi na gwamnan jihar Borno.
Wannan ya sa kungiyoyin matasa suke cewa ba za ta sabu ba a wannan karon duk wanda ya guji talakawa to ba za su bari a sake zabar sa ba, lamarin da ake ganin yana gaskata maganar gwamnan jihar Bornon ne. Saboda haka ne ma matasan suka bukaci gwamnonin da sauran zababbu wakilai da su tabbatar sun yi adalci tare da yin ayyukan da za su kyautata rayuwar talakawa, ta hakane kawai za'a magance matsaloli da ake fuskanta a Arewacin Najeriya.
Malam Ibrahim Yusuf wanda aka fi sani da Three Thousand daya daga cikin shugabannin matasan Arewacin Najeriya ne masu fafutukar tabbatar da dalci wa al'umma. Shi ma ya go yi bayan matakin kusantar masu mulki ga wadanda suke mulka, muddin ana son tsaman lafiya.
A baya ma dai kungiyoyin fararen hula da talakawa sun yi irin wannan gargadi to amma babu wani canji na azo a gani, musamman a yankin Arewacin Najeriya, inda zababbun shugabanni ke buya daga ganin talakawan su har sai lokacin zabe ya karato suke bayyana.
Mawallafi: Al-Amin Sulaiman Muhammed
Edita: Usman Shehu Usman