1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rashin tsaro da makomar ilimi

June 18, 2021

Kwana guda bayan sace daliban makarantar kwalejin gwanatin tarayya da barayi sukayi a birnin Yawuri na jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, rahotanni na nuni da cewa an kubutar da yaran bayan musayar wuta.

https://p.dw.com/p/3vC4P
Weltspiegel 03.03.2021 | Nigeria Zamfara | Freilassung entführter Schulmädchen
Ba dai wannan ne karon farko da aka kwashe dalibai a makarantar kwana a Najeriya baHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Rahotanni sun nunar da cewa dakarun sojojin Najeriyar sun yi wa 'yan bindigar kawanya ne a maboyarsu da ke Dajin Makuku da kuma Dirin Daji,, inda kuma suka samu nasarar ceto daliban. Har lokacin hada wannan rahoton dai, DW ba ta shaida dawowar yaran ba. Tuni dai iyayen yaran ke ta bayyana fatan da suke da shi ga 'ya'yansu. Kawo yanzu dai bayan rufe makarantar, ba a iya tantance iya adadin daliban da 'yan bindigar suka tafi da su ba, a cewar shugaban makarantar. Kokarin jin ta bakin hukumomin tsaro a jihar Kebbi bai yi nasara ba. A cewar kwamishiniyar shari'a ta jihar, Ramatu Adamu Gulma a watannin baya jihar ta aiwatar da wata doka ta hukunta masu garkuwa da mutane.