1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rex Tillerson zai kai ziyara kasashen Afirka

Yusuf Bala Nayaya
March 2, 2018

A makon me zuwa ne sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson zai kai wata ziyara kasashen Afirka kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta bayyana a ranar Alhamis.

https://p.dw.com/p/2tYzr
USA Rex Tillerson in Malaysia
Hoto: Getty Images/AFP/M. Vatsyayana

Ziyarar da ke zama ta farko a wannan nahiya tun bayan da Shugaba Donald Trump ya hau karagar mulki.

Tillerson zai ziyarci manyan biranen kasashen Chadi da Djibouti da Habasha da Kenya da Najeriya, a ziyarar da zai kai tsakanin ranakun shida zuwa 13 ga watan nan na Maris kamar yadda Heather Nauert da ke magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen na Amirka ta bayyana a ranar Alhamis.

Wannan ziyara dai ta Tillerson na zuwa ne bayan da mai gidansa Trump a watan Janairu ya bayyana kasashen na Afirka a matsayin kofar shadda, ana kuma sa ran a lokacin ziyarar ya gana da shugabanni na kasashen da shugabanni a kungiyar AU inda za su mayar da hankali kan batutuwa da suka shafi tsaro da kasuwanci da shugabanci nagari.