1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ribar huldar Najeriya da Faransa

Usman ShehuFebruary 27, 2014

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande na ziyara a Tarayyar Najeriya, domin halartar bukukuwar cika shekaru dari da hadewar kasa da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/1BGwN
Frankreich Präsident Hollande einjähriges Amtsjubiläum 16.05.2013
Hoto: P. Kovarik/AFP/Getty Images

Baya dai ga batun tsaro, Shugaba Francois Hollande zai yi amfani da wannan dama wajen karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, musamman na kasuwanci. Ba safai ne shugaban Faransa yake kai ziyara a Tarayar Najeriya ba. A cikin tarihi ma dai ziyarar ta Francois Hollande, ita ce ta biyu baya ga wacce Jacques Chirac, ya kai a shekara ta 1999.

Amma dai cin tuwon kishiya ne wanda masu iya magana kan ce ramako, domin kuwa sau biyu shugaban Tarayyar Najeriya ya yi tattaki zuwa Paris, domin halartar tarurrukan da Faransa ta shirya. A cewar Forfesa Boubé Namaiwa, na jami'ar Anta Diop da ke Dakar na Senegal baya ga bukuwar cikan Najeriya shekaru 100 da kafuwa, Holland da kasarsa ce za su fi cin gajiyar ziyarar.

Nigeria Abuja Militärparade
Hoto: DW/U. Musa

"Wani ma abinda ya ke shigewa wa mutane da dama duhu sune cewar, Tarayyar Najeriya ce ke sahun gaba a kasashe da Faransa ke saye da sayarwa tsakaninsu". A cewar sadiq Abba, darektan yada labarai a mujallar Jeune Afrique l'intelligent da ke da cibiya a birnin Paris, "dangantakar kasuwanci da fadar mulki ta Abuja zai bai wa tattalin arzikin Faransa damar murmurewa".

Ita dai Tarayyar ta Najeriya tana iyaka ne da kasashen da Faransa ta taba yi wa mulkin mallaka, wato kasashen Nijar da Kamaru da Cadi da kuma Jamhuriyar Benin. Akasarinsu dai na fuskantar barazanar tsaro da kuma fashin jiragen ruwa a tekun Gini. Saboda haka ne farfesa Boubé ya ke ganin cewa, "kaddamar da wannan yaki ba tare da Najeriya, tamkar dai a yi tuya ne a manta da albasa"

Ita dai Faransa za ta bai wa gwamnatin Tarayyar Najeriya bashin Euro milliyan 650, domin ta yi amfani da su wajen magance matsalar karancin wutar lantarki da ke addabar tattalin arzikin Najeriya.

Mawallafi:Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Usman Shehu Usman