1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riciki da yawan al'uma a Afirka sun mamaye jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
June 23, 2017

https://p.dw.com/p/2fH4D
Zentralafrikanischen Republik Bangui - Reifen brennt in zerstörter Moschee
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Blackwell

A labarin da ta rubuta mai taken "Kundin zaman lafiya" jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce gwamnatin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kungiyoyin da basa ga maciji da juna  a kasar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Rome na kasar Italiya.

A karkashin shiga tsakanin wata kungiyar fafutukar zaman lafiya da kare hakkin jama'a ta mabiya darikar Roman Katolika mai suna Sant Egidio aka cimma wannan matsaya. A ranar Litinin da maraice ne dai kungiyoyin tawaye da ke dauke da makamai da wakilan gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar suka ayyana tsagaita wuta, wanda zai kasance a kasarkashin sa idon al'umomin kasa da kasa.

Zentralafrikanische Republik Freilassung von Kindersoldaten
Hoto: Reuters/E. Braun

A shekara ta 2013 ne dai yakin ya barke a wannan kasa ta Afirka. Mayakan tawaye na Seleka daga arewacin kasar da akasarinsu musulmi ne, sun yi taho mu gama da gwamnati a birinin Bangui. Magoya bayan gwamnati wadanda akasarinsu Kiristoci wato Anti Balaka, sun hade a wannan yakin da ya yi sanadiyyar rayukan mutane masu yawa, yayin da dubban wasu kuwa suka tsere daga matsugunnansu. Yanzu haka dai akwai dakarun kasa da kasa karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya na MINUSCA kimanin dubu 13 a girke a kasar, a wani mataki na tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Daga batun cimma sulhu a Afirka ta Tsakiya sai kuma matsalar karuwan yawan jama'a a nahiyar Afirka. Jaridar Der Spiegel ta ruwaito yadda karuwar haihuwa tsakanin al'umar Afirka ke kara razana duniya dangane da makomar nahiyar a nan gaba. Na baya-bayannan da ya fi daukar hankali dai shi ne tsokacin Björn Höcke, masani kan batutuwa da suka jibanci halittar dan adam. Ya danganta karuwar matsalar 'yan gudun hijira a Turai da abin da ya kira cunkoson jama'a a Afirka.

Zentralafrikanische Republik Freilassung von Kindersoldaten
Hoto: Reuters/E. Braun

Ya kwatanta yadda turawa ke tsara rayuwarsu tare da nazari kafin su yanke hukuncin haihuwa, da kuma yadda al'umar Afirka ba sa daukar wani mataki na kariya balle kayyade haihuwar. A kan haka ne ya ce matukar Turai za ta ci gaba da marabtan karuwar al'umar, to ko shakka babu al'umar Afirka ba za su dauki wani mataki na takaita hauhuwa ba. To sai dai akwai sabanin ra'ayi dangane da wannan matsayi na shi, domin kwararru na nuni da cewar a yanzu haka ana samun koma baya a bangaren haihuwa a Afirka. Duk da cewar har yanzu ana samun karuwar al'uma a wasu kasashe matalauta kamar jamhuriyar Nijar. Kuma ko kadan karuwar al'uma Afirka ba shi da wata nasaba da tsarin 'yan gudun hijirar Turai.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung sharhi ta yi dangane da matsalar yunwa a Afirka da kuma irin tallafin da ya kamata a bayar domin shawo kan matsalar ganin cewar, ba bakuwar aba bace. Jaridar ta ci gaba da cewar shekaru masu yawa, al'umomin duniya ke kira ga masu bada gudunmawa. A kullum dai martanin baya zuwa daidai da matsalar da ke kewayen Afirkar.

Äthiopien Ein unterernährtes Kind wartet mit seiner Mutter im Krankenhaus
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Morison

Akan nuna hotuna ta majigi da alluna a titunan kasashe daban-daban domin yada irin wahar da nahiyar ke ciki da al'umarta. Sai dai a kullum gudummowar da ake bayarwa bata taka kara ta karya ba, inda sannu a hankali yake ci gaba da yin tafiyar hawainiya, wanda ake dangantawa da karin matsin rayuwar jama'a a nahiyar. Ayar tambaya anan ita ce, duk da yawan kiraye-kiraye don kawo tallafi da ake yi shekara da shekaru, me ya sa har yanzu kwalliya ba ta biyan kudin sabulu?