Rikici a Taraba ya jawo salwantar rayuka
June 15, 2014Talla
Tashin hankalin dai kamar yanda shaidu suka tabbatar ya samo tushensa ne bayan da aka zargi matasan kabilar Jukun da lalata wuraren sayar da wayoyin sadarwa mallakin Hausa-Fulani mazauna garin, yayin kuma da su Hausawan suka nemi dalili, sai fada ya kaure.
A zantawarsa da Wakilinmu na Yolan jihar Adamawa Muntaqa Ahiwa, wani mutum da ya shaida faruwar abin ya ce ya ga gawawwaki da yawa kana an kone gidaje da dama sakamakon barkewar rikicin.
Yankin kudancin Taraba dai yanki ne da ya yi kaurin suna wajen samun rigingimun addini da na kabilaci, rigingimun da ke zama sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Mawallafi: Muntaqa Ahiwa/Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe