1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya ki ci, ya ki cinyewa a Bangui

December 23, 2013

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ana ci gaba da fuskantar hare-hare daga masu dauke da makamai masu gaba da juna

https://p.dw.com/p/1Afo6
Hoto: picture alliance/AA

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sati biyu bayan arangama tsakanin 'yan tsohuwar kungiyar Seleka da mayakan sa kai masu adawa da yan kabilar Balakas, Babban Asibitin birnin Bangui ya cika makil da mutanen da suka ji rauni ta harbin bindiga ko kuma sara da adda.

Daga cikin harabar asibitin, 'yan kungiyar agaji ta Medecin Sans Frontieres sun kafa wata runfa, inda suke karbar wadanda suka ji rauni sakamakon rikice-rikicen da ya afkawa birnin na Bangui tun daga daran biyar ga watan Disamba.

A karkashin wannan runfa akwai a kalla mutane 20 da suka ji ciwo mai tsanani kwance bisa wasu kananan katifu da aka shinfida ana kula da su, inda wasu da dama da ganin su, sun gaji kuma da kyar suke magana, kamar wani mutun mai suna Arsene wanda aka harba da bindiga tun ran biyar ga watan nan na Disamba.

Zentralafrika Unruhe Protest am 23.12.2013
Hoto: MIGUEL MEDINA/AFP/Getty Images

"Ni ina gudu ne har na kai inda zan tsere suka harbeni a kafa ta, wajejen idan sau na na dama."

Amma kuma Arsene ya ki fadar wadanda suka harbe shi, sabili da tsoron abun da zai biyo baya.

Shi ma Yussuf da ke zaune a wata anguwa da ke arewacin birnin na Bangui an harbe shi ne da harsashi a wannan rana, a dai dai lokacin da yake kokarin barin anguwar.

"A ranar biyar ga watan Disamba ce dai masu adawa da kabilar nan ta Balakas da suka fito daga wajejen Gobongo da kuma anguwar da ke kallon wajan, a lokacin kuma akwai wani gungun mutane da suka je anguwar domin su yi kwace ga yan anguwar, muna zuwa ne muka hadu da su kan hanya, sai suka bude mana wuta. To cikin muna gudu ne sai kawai na ji harsashi ta baya ga cinya ta, inda nan take kashin ya karye to tun lokacin nan washe gari aka kawo ni nan asibiti."

Kamar Arsene da Yussuf, daruruwan mutanen da suka samu rauni ne ke samun kulawa ta musammam daga yan kungiyar Medecin Sans Frontieres, wanda suka taimakawa babban asibitin da kayan aiki. Marie Elisabeht Ingres, mataimakiyar shugabar kungiyar agajin ta Medecin Sans Frontieres cewa ta ke.

Flüchtlinge Zentralafrikanische Republik
Hoto: 2013 Marcus Bleasdale/VII for Human Rights Watch

'A nan wannan babban asibitin akasari muna karbar mutanen da suka ji rauni suke bukatar kulawa ta gawgawa, dan haka a halin yanzu bana iya bada adadin mutanen. Amma sun kai kusan dari hudu, domin mun fuskanci shigowar masu rauni da dama tsakanin ranar biyar zuwa shidda ga watan nan, sai kuma wasu masu zuwa da muka samu a yau din nan."

Ga bakidayan ma'aikatan wannan asibiti sun dukufa wajen kula da mutanen da ake kawowa sakamakon harbin bindiga ko sara da adduna. A cewar darektan wannan asibiti da ke birnin Bangui na Jamahuriyar Afrika ta Tsakiya, suna karbar ma jinyata ne ba tare da banbancin addini ba.

A farkon harbe-harben dai a ranar biyar ga wata kadai, an samu a kalla mutane 92 da suka mutu, yayin da wasu 155 suka jikkata. Inda a cewa yan kungiyar kare yancin dan adam ta Amnesty International da ke kasar a halin yanzu, adadin wadanda suka mutu ko suka ji rauni, ya zarta dubunnai. Tuni dai wasu suka fara tunanin a raba kasar kudu da arewa muddin dai aka kasa shawo kan matsalar, abun da kakakin shugaban kasar Djotodia ya ce sam ba za ta sabu ba, domin Jamahuriyar Afrika Tsakiyar kasa daya ce.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Usman Shehu Usman