Rikicin ƙasar Mali
December 2, 2012Talla
Shugabannin ƙasashen Nijar da Mali sun baiyana takaicin su dangane da ja da baya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi akan matakin da ƙasashen suke jiran a ɗauka akan yan tawayen da suka mammaye yankin arewacin Mali kusan watanni tara.
Shugaban gwamnatin wucin gadin na Mali wanda yanzu haka ya ke yin ziyara aiki a Nijar ;da shi da Takwaransa Mahamadou Issoufou sun yi nadama a game da yadda ƙasashen duniyar ke jan kafa wajan ba da haɗin kai ga ɗaukar mataki soji akan yan tawayen na Mali.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal