1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ƙasar Siriya

April 19, 2012

Amurka ta ce ƙasar Syriya ta gaza wajen cimma ƙudurorin shirin wanzar da zaman lafiya wanda tsohon shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ke jagoranta.

https://p.dw.com/p/14hpf
epa03139216 A handout picture released by Syrian Arab News Agency SANA, shows Syrian President Bashar Al-Assad (R) listening to UN Arab League envoy Kofi Annan (L) during their meeting, at Syrian presidential palace in Damascus, Syria, 10 March 2012. Annan arrives in Damascus on 10 March and is expected to call for talks between the government and the opposition in a bid to end the year-long violence. EPA/SANA HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Shugaba Bashar al-Assad da Kofi AnnanHoto: picture-alliance/dpa

Jakadar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Susan Rice ce ta bayyana haka inda ta ƙara da cewar duk da an ɗan tsagaita rikicin bayan da wa'adin tsagaita wuta ya fara aiki ranar sha biyu ga wannan watan, an cigaba da jefa bama-bamai a garin Homs da wasu birane.

Rice ta ƙara da cewar baya ga haka ƙasar ta Syria ta gaza biyan buƙatun waɗanda rikicin ƙasar ya ɗaiɗaita wanda aka kwashe kimanin watanni sha uku ana gudanarwa.

Da ya ke sharhi kan wannan batu, wani jigo a kwamitin kawo sauyi na demokraɗiyya A Syria Haytham Manna ya ce wasu marasa son zaman lafiya ne ke koƙarin yin maƙarƙashiya ga shirin na wanzar da zaman lafiya a ƙasar ta Siriya

Ya ce 'wasu mutanan na fatan ganin shirin na Kofi Annan ya samu naƙasu, muna buƙatar ganin an yi amfani da shirin domin zai taimaka wajen samun zaman lafiya, muna kuma buƙatar Rasha ta taimaka wajen matsawa mahukuntan Damascus lamba da su mutunta shirin na tsagaita wuta'.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar