1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin cikin gida na 'yan tawayen Siriya

Usman ShehuJanuary 7, 2014

Aƙalla 'yan tawayen 34 aka kashe a Idlib a faɗan da aka gobza tsakanin ƙungiyoyin 'yan tawayen .

https://p.dw.com/p/1AmLr
Irak Gewalt Ramadi Falluja Islamisten Militanten Al Qaida Al Kaida
Hoto: Reuters

An ba da rahoton cewar ana gwabza faɗan ne tsakanin ƙungiyoyin 'yan tawayen masu kishin adini a garin Idlib tsakanin gungun 'yan tawayen da ke ƙiran kansu 'yan tawayen Siriya na haƙiƙa, da kuma ɓangaren da ke iƙirarin yin jihadi. A baya dai duk waɗannan ƙungiyoyi sun haɗu ne suna yaƙar gwamnatin Bashar Al Assad.

A wani lamarin da ya shafi ƙasar ta Siriya kuma, hukumar kula da kare yancin ɗan adam ta MDD ta ce daga yanzu ta daina rubuta wani ƙarin alƙaluman mutanen da ke mutuwa a Siriya. Hukumar ta ce, a halin da ake ciki ta gaza gane gaskiyyar abin da ke faruwa dangane da rahotannin da ke karo da juna a kan addadin. Hukumar ta MDD ta ce daga alƙaluman watan Yulin bara da ta ba da rahoton cewar mutane 100, suka mutu a rikicin na Siriya, ba ta sake rubuta wani sabon sakamakon ba. Babbar matsalar dai ita ce, bisa hatsarin yaƙin ƙungiyoyin masu zaman kansu ba sa samun isa inda ake tashin hankali.

Mawallafi : Usman Shehu
Edita : Abdourahamane Hassane