1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin gabashin Ukraine na kara rincabewa

January 13, 2015

Mutane hudu sun hallaka a sabon rikicin da ya barke cikin yankin gabashin kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/1EJcl

Rahotanni daga gabashin kasar Ukraine sun tabbatar da mutuwar fararen hula uku da soji daya yayin fafatawa da 'yan aware a wannan Talata.

Rundunar sojin kasar ta ce akwai wasu sojoji 10 da suka samu raunuka lokacin dauki ba dadin da 'yan awaren masu goyon bayan Rasha kusa da garin Donetsk.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal