1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

December 13, 2013

Ranar jumma'a wasu masu tayar da ƙayar baya sun hallaka aƙalla mutane 27 kuma al'ummar na kwana waje dan kare dukiyoyinsu da kuma tsira da rayuwarsu

https://p.dw.com/p/1AZaB
Zentral Afrikanische Republik UN Truppen nach Bangui
Hoto: PACOME PABANDJI/AFP/Getty Images

Majiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce wata ƙungiya mai tada ƙayar baya ta kashe mutane 27 a wani ƙauye da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a wani harin da ke daɗa nuna ƙalubalen da dakarun Faransa ke fiskanta wajen daidaita ƙasar.Ƙungiyar wadda ake kira Anti-Balaka ta kashe mutanen ne a Bohong wani ƙauyen da ke da tazarar kilometa 75 daga yancin yammacin garin Bouar a Arewacin ƙasar.

Mohammadu Bigirima wani mazaunin Bouar ɗin ne da ke yankin arewacin ƙasar kuma ya ce suna zama cikin matuƙar fargaba:"Mu haka a yanzu, a waje muke kwana saboda muna tsoron rayukanmu da dukiyarmu da ke waje, muddin ka koma ɗaki ka kwanto, to za a fasa ma ka shagunanka, kuma kai ma za a zo a nemi kashe ka da kai da iyalanka, to ka ga dan haka ya zama wajibi ka fita, ɗan makamin da ka ke da shi ka fitar da shi ka kare kanka.Dakaraun Faransa sun kai 1,600 kuma kamfanin dillancin labarun Reuters ya ce sun fara samar da zaman lafiya a babban birnin ƙasar wato Bangui

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: AbdourahAmane Hassane