1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya

November 23, 2021

A yayin da ake ci gaba da fuskantar ta'azzarar rikicin cikin gida tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya inda ta sake dage babban taro na kasa har ya zuwa watan Fabrairu na badi.

https://p.dw.com/p/43Mqz
Nigeria, Abuja: Präsident Muhammadu Buhari begrüßt seine Unterstützer
Hoto: Reuters/B. Omoboriowo

Ya zuwa yanzu dai kusan rassan jam'iyyar na jihohi 22 cikin kasar na fuskantar rikicin cikin gida na shugabanci da wakilcin jam'iyyar da ke zaman ta kan gaba a Najeriya.

Kuma sau uku ke nan APC ke dage kokari na babban taron da take fata na iya kai wa ga zaben shugabannin da suke shirin daukar jam'iyyar ya zuwa ga yakin neman ci gaba bisa mulkin kasar anan gaba. To sai dai babu zato ba tsamanni shugabancin jam'iyyar na riko ya sanar da dage babban taron zuwa watan Fabrairu na badi.

Karin Bayani: Najeriya: Rikicin siyasa da zaben 2023

Abuja, Partei Kongress der in Nigeria regierenden APC
Hoto: DW/U.Musa

Bayan wata ganawa da shugaban kasar Muhammadu Buhari dai wasu gwamnonin jam'iyyar da suka hada da shugaban jam'iyyar na riko Mai Mala Buni da shugaban gwamnonin APC Atiku Bagudu gami da gwamnan jihar Jigawa sun ce shugaban kasar ya amince da bukatar gwamnonin jam'iyyar na dage babban taron da nufin neman kintsi.

Idan gwamnonin sun yi nasarar shawo kan shugaban kasar zuwa dage babban taron dai, daga dukkan alamu suna da jan aikin sauya tunanin fadar ga sauya salon zabe na masu takara a zabukan kasar da ke tafe. Duk da adawa daga gwamnonin dai 'yan majalisar tarrayar kasar sunyi tsaiwar gwamin jaki bisa zabin yar tinkin a matsayin hanyar fidda masu takara a zabukan kasar da ke tafe.

Jam'iyyar APC dai na fatan iya warware rikicin a lokaci na iya bada damar kaddamar da sabon kokari na burge 'yan kasar da ke shirin yanke hukunci bisa rawar da ta taka a shekaru takwas na farkon fari.