1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin APC kan matakin matasan jam'iyyar

Uwais Abubakar Idris ZMA
December 3, 2021

A Najeriya shugabanin APC mai mulki sun yi watsi da wasu matasan jam'iyyar da suka ayyana kansu a matsayinsu shugabanni bayan ballewa tare da kafa majalisar zartaswarsu.

https://p.dw.com/p/43oQ5
Nigeria, Abuja: Präsident Muhammadu Buhari begrüßt seine Unterstützer
Hoto: Reuters/B. Omoboriowo

Allah wadai da ma cewa basu yarda ba da shugabanin jamiyyar APC suka yi a kan wannan bangare da ya balle wanda shi ne karon farko da suke maida murtani a kan abinda ya faru da ya nuna daukan sabon salo a rigingimun da suka dade suna fuskantara jamiyyar ta APC duk kuwa da ikirari na rijistar sama da mutane milyan 60 a Najeriyar.

Darewa gida biyu da jamiyyar ta yi inda wasu matasan karkashin jagorancin Mustapha Audu da ya ayyana kansa a matsayin shugaban jamiyyar.

Kama daga matakin kanana hukumomi ya zuwa jiha da ma wasu ‘yan majalisar Najeriyar jamiyyar ta APC ke fama da rigingimu na cikin gida, inda ta kai ga wasu runtumawa zuwa kotu irin su Sanata Kabiru Marafa na jihar Zamfara. Da yace babu wanda ya isa ya yi musu "ture kaza kwashe kwai".

Bisa ga abubuwan da ke faruwa ya nuna a fili cewa ‘yan siyasar Najeriyar basa koyon darasi ga abin da ya faru a baya, sanin yadda rikici ya kai jamiyyar adawa ta PDP a yanzu ga APC ta kama, abin da ke nuna bukatar waiwaye da a kan ce adon tafiya.