1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Koriya Ta Arewa da Ta Kudu

July 24, 2010

Gwamnatin Pyongyang ta ce za ta bayyana yaƙin ƙwato 'yancinta daga barazana da Amurka da Koriya Ta Kudu ke yi ma ta

https://p.dw.com/p/OTcI
Shugaban ƙasar Koriya Ta Arewa Kim Jong IlHoto: AP

Ƙasar Koriya ta Arewa ta yi gargaɗin cewa, za ta bayyana yaƙi na ƙwato 'yancin ta daga Amurka da kuma Koriya Ta kudu, bakin rai bakin fama, saboda abinda ta kira barazana da kuma take-taken da ta ce ƙasashen biyu suke yi ma ta.

Jum kaɗan dai bayan sanarwa da suka bayyana a yau, Amurka ta mayar da martanin ta na mai cewa ba za ta shiga yin yaƙin cacar baka ba da Koriya Ta Arewar, ko kuma neman tsokana.

Abinda ta ce suke buƙata ga hukumomin na Pyongyang, shi ne abu na zahiri da zai taimaka ga warware matsalar da ake ciki kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Amurka mista Crowley ya sanar.

A gobe ne dai idan Allah Ya kaimu aka shirya sojojin ruwa na Amurka da na Koriya Ta Kudu za su gudanar da wani atisaye, abinda Koriya Ta Arewa ke kallon wata barazana ce.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Mohammad Nasiru Awal