Rikicin Libiya ya lakume rayuka fiye da 100

Kasa da makonni biyu da soma kai hare-haren neman kwace ikon birnin Tripoli ba tare da ya yi nasarar ba, babban kwamandan sojin ‘yan tawaye, Janar Haftar ya gana da Shugaban Masar Abdelfattah Al-sisi.

Ziyarar da ke zuwa jim kadan bayan kakkabo wani jirgin yakinsa a sararin samaniyar Tripoli, tare da kame wasu gwamman sojinsa a matsayin fursunonin yaki. Masu fashin baki sun ce ziyarar ta gaisuwa ce da kuma rokon iri. Sai dai ziyarrar na zuwa ne a daidai lokacin da Haftar ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan ya dakatar da hare-haren da ya ke kai wa kan abokan hamayyarsa.

Mutum akalla 120 ne suka mutu wasu fiye da 500 suka jikkata a sanadiyar rikicin kwace ikon birnin Tripoli na kasar Libiya kamar yadda wata sanarwar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ke cewa.
Rahotanni masu dangantaka