1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siriya na cigaba da rincaɓewa

January 19, 2013

Hukumar kare haƙƙoƙin bani Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta koka da ƙaruwar mace-mace a Siriya.

https://p.dw.com/p/17NQ9
A damaged building is seen in Homs January 19, 2013. Syrian President Bashar al-Assad's forces were attacked and surrounded the Khaldiyeh area in Homs, the Free Syrian Army said. REUTERS/Yazan Homsy (SYRIA - Tags: CONFLICT SOCIETY POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

A hare-haren da ɓangarorin da ke hamayya da juna a ƙasar Siriya ke yi,rahotani sun nuna cewar kimanin mutane 119 ne su ka rasa rayukansu a ranar jiya Juma'a kaɗai daga ciki har da wasu 'yan jarida guda biyu da suka haɗa da Yves Debay ɗan ƙasar Faransa da kuma Mahamed Hourani da kewa gidan talabijan na Aljazira aiki. Shugabar hukumar Kare haƙƙoƙin bani Adama ta Majalisar Dinkin Duniya,Navi Pillay,ta ce bisa ga ƙiddidigar da suke yi adadin mutane dubu 60 da aka bayar na waɗanda suka rasa rayukansu,ya lunka.

Hasali ma Pillay ta ce in can farko mutane dubu ne ke rasa rayukansu a kowane wata,to a yanzu adadin ya kai kimanin dubu 5 a kowane wata. Ko a jiya Juma'a dubban mutane ne suka gudanar da zanga zanga kamar kowace Juma'a to amman ta jiya don nuna goyon bayansu ga ɗaliban jami'ar Alepo da a kawa ruwan bama-bamai.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi