1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Ivory Coast

Zainab A MohammadOctober 7, 2005

Kungiyar AU tace shugaba Gbagbo zai cigaba da kasancewa shugaba

https://p.dw.com/p/BvZ5
Hoto: AP

A wani abunda ke zama koma baya way an tawayen kasar Ivory coast,shugabannin kungiyar gamayyar Afrika Au,sun sanar dacewa shugaba Laurent Gbagbo zai cigaba da kasancewa kan karagar mulki na tsawon watanni 12,bayan waadinsa ya kare a karshen wannan watan.

Bisa dukkan alamu dai wannan sanarwa ta kungiyar ta Au mai wakilan kasashe 53,kungiyar da kuma akewa kallon mai samarda sulhu a nahiyar Afrika,zai iya tayar da rikice rikice na siyasa.

Tun da aka fara shakkun yiwuwan gudanar da zabe ranar 30 ga wannan wata nedai,alummar kasar ta Ivory Coast mai arzikin koko,suka fara kasancewa cikin zulumi dangane da barkewan sabon rikici.

A Sanarwan bayan taronta daya dauki saoi 4 yana gudana,komitin sulhu da tsaro na kungiyar ta gamayyar Afrika,taron daya samu halartan shugaba Thabo Mbeki na Afrika ta kudu,da shugaba Olusegun Obasanjo dake jagorantar kungiyar,na bayyana cewa shugaba Bagboy a bada wasu madafan iko wa sabon prime minister,wanda kuma zai samu cikakken madafan iko kan ministocinsa.

Bugu da ,kari sanarwar ta jaddada muhimmancin hadewar kasar ta Ivory Coast wadda ta dare biyu ,cikin gaggawa,wanda kuma bazaa iya cimma nasaran hakan ba saida ingantaccen sulhu tsakanin bangarorin biyu.

Dayake karantawa manema labaru sanarwar bayan taron,Commission sulhu da tsaro na kungiyar ta Au Said Djinnit yace Shugaba Laurent Gbagbo,zaici gaba da kasancewa kan kujerar mulki har tsawon watanni 12 masu gabatowa,ayayinda zaa nada sabon prime minister wanda zai zama amintacce wa dukkan bangarorin dake gaba da juna a kasar ta Ivory coast,kana gwamnati zata cigaba da aiwatar da harkokinta na mulki dangane da yarjeniyoyi da aka cimma a Linas-Marcoussis da Pretoria,kuma sabon prime ministan zai mallaki cikakken madafun iko kan dukkan ministocinsa.

To sai dai ana ganin wannan sanarwa zata iya harzuka yan adawan kasar,wadanda tun a baya sukayi gargadin cewa dole Shugaba Bagboy a sauka daga kujerarsa a karshen waaadinsa na 30 ga wannan wata,tare da nada gwamnatin rikohar zuwa lokacin da zaa gudanar da zabe.Kakakin yan adawan ya bayyana cewa bai samu wannan zartarwan bayan taron na Au ba,inda ya nanata cewa suna kan bakansu na bukatar shugaba Gbagbo ya sauka daga kujerar mulkin nasa a karshen wannan wata.

Amadou Kone dake zama babban mataimakin shugaban yan adawa Guillaume Soro,ya kara dacewa Shugaban Ivory coast din ne yaki aiwatar da dukkan yarjejeniya da aka cimma,adangane da haka babu yadda zai iya gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Shi kuwa kakakin Laurent Gbagbo Desire Tagro, ya tabbatar dacewa Gbagbo zaicigaba da kasancewa shugaban kasa ,tare da dukkan madafan iko da kundun tsarin mulki ta bashi,har sai an gudanar da zabe.

A makon daya gabata nedai kungiyar cinikayya ta yammacin Afrika watau ECOWAs ta gudanar da taro akan rikicin Ivory Coast din a Abujan Nigeria,inda ta zartar dacewa zata bukaci AU tayi laakari da garon bawul a gwamnatin kasar.

Shi kuwa Shugaba Gbagbo cewa yayi bazaar iya gudanar da zabe a ranar 30 ga wata kamar yadda a tsayr a baya ba,saboda yan adawa dake rike da arewacin kasar tun shekaru uku da suka gabata sunki kwance damarar yaki.

Ivory Coast mai zama kasa ta farko a jerin kasashe masu arzikin koko a duniya dai,ta fada yakin basasa tun daya watan satumban 2002,lokacin day an adawan kasar suka cafke arewacin kasar,sakamakon yunkurin kifar da gwamnati da baiyi nasara ba,tun lokacin kasar ta cigaba da kasancewa a rabe,da kudanci a hannun gwamnati.