1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siyasa a Liberia

Yahouza SadissouDecember 13, 2005

Gwamnatin Liberia ta buda binciken a kan jita jitar yunkurin juyin mulki.

https://p.dw.com/p/Bu3S
Hoto: AP

Gwamnati kasar Liberia ta bada sanarwar buda bincike, domin gano gaskiyar magana, a game da, rundamin juyin mulki, da a ka zargi wasu sojoji da shiryawa, kwanaki kadan bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa.

Magoyan bayan dan takara da sha kasa a wannan zabe, wato Gerorges Weah, na ci gaba da shelar an tabka magudi ga zaben.

Tsakanin ranar lahadi ta litinin sun shirya zanga zanga da dama don jadada wannan matsayi.

Shi kansa Georges Weah, mai farin jini mussaman daga wajen matasa, ya gabatar da jawabi ranar da a ka shirya zanga zangar inda ya jaddada wa magoya baya nasa cewar lalle babu shaka shi ya ci zabe a ki mada kwace.

Wannan kalamomi na Georges Weah, na kara hadasa rudani, a kasar Liberia, da wasu ke zullumin cewa zata fada wani saban rikici.

Kasancewar halin digirgire da zaman lahiyar kasar ke ciki ba mamaki, wasu sojoji su yi anfani da wannan dama, domin su shirya juyin mulki.

To saidai, masharahanta na nuni da cewa, sabuwar shugabar kasar da a ka zabe wato Ellen Sirleaf Johnson, wacce a yanzu ke cikin ziyara aiki a kasar Amurika, na da cikkaken goyan baya daga kasashe dunia, mussaman a Kungiyar Taraya Afrika, da ita kanta majalisar Dinkin Dunia, ga kuma tabaraki da ta samu daga kasashe kamar su Amurika da Faransa.

Aiwatar da juyin mulki cikin wannan hali, zai iya zama kayar wuya, ga masu bukatar hakan.

Wakilin Majalisar Dinkin Dunia a kasar Liberia, Allen Doss, tunni ya bayana samarwa mai yi Allah wadai da wannan sabuwar fitina, ya kuma kira ga jam´iyar CDC ta Georges Weah ,da ta ladabtar da magoya bayan ta.

Gwamnati rikwan kwarya ta kiri taron majalisar ministoci domin nazari a kan wannan saban yanayi da kasar ke shirin fadawa.

Sanarwar karshe taron da ministan watsa labarai ya karanto, ta tabatar da daukar matakan da su ka dace, don maido da zaman lahia.

Ministan watsa labarai, da ya hiddo sanarwar fara binciken, ya ce akwai ministoci 2 ,da ke da hannu a cikin yunkuri juyin mulkin, saidai, bai bayyana sunayen su ba.

A nasa bangare, Georges Weah a wata hira da yayi, da gidan redion King mallakar sa, ya zargi jami´an tsaro da cin zarafin magoya bayan sa, a sakamakon arangamar da su ka yi, ranar jiya, ya kuma yi watsi da zargin da jami´an tsaro ke masa, na shirya juyin mulkin.

Ministan shari´a ,Liberia da shima masu zanga zangar su ka abkawa motar sa, ya tabatar da daukar matakan gurfanar da dukan wanda a ka samu da hannu a cikin lalata dukiyar jama´a a zanga zangar da magoya bayan Georges Weah su ka shirya.

Ranar 16 ga wata da mu ke ciki ne ta kamata a rantsar da sabuwar shugabar Liberia, to saidai Georges ya sha alwashin cewa babu batun wannan rantsuwa muddun ba a kamala sauraran karan da jami´yar CDC ta shigar ba, a game da zargin magudi.