1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar Shekau da janye sojojin Faransa a Sahel

Mohammad Nasiru Awal LMJ
June 11, 2021

Takaddamar kamfanin Twitter da gwamnatin Najeriya da mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram, sun dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3uljs
Twitter Logo
Gwamnatin Najeriya ta garkame kamfanin sadarwar zamani na Twitter a kasarHoto: picture-alliance/AP Images/STRMX

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci kan dakatar da aikin kamfanin sadarwar zamani na Twitter a Najeriya, matakin da ta fara da cewa ya yi tsauri ya kuma janyo kace-nace. Sai dai kuma ya sha yabo daga tsohon shugaban Amirka Donald Trump. Jaridar ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba zai yarda a hana shi furta albarkacin bakinsa ba, musamman daga wani kamfanin kasar Amirka. Yanzu kamfanin Twitter ya shaida haka a Najeriya kasa mafi yawan al'umma a Afirka, bayan da kafar sada zumuntan ta goge wasu kalaman da Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa bisa dalilan cewa suna iya haddasa rikici. Sai dai 'yan Najeriya musamman mazauna kasashen waje da jam'iyyar adawa, sun soki matakin da cewa wani yunkuri ne na rufe bakin al'umma a kasar da shafukan sada zumunta na zamanin ke taka gagarumar rawa wajen saurin yada labarai ko dai na gaskiya ko na kanzon kurege.
Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta leka Najeriyar amma kan batun tsaro tana mai cewa jagoran Boko Haram Abubakar Shekau ya rasu, bayan ya tayar da bam da ya daure a jikinshi lokacin da mayakan wata kungiyar ta'adda ta yi masa kawanya. Jaridar ta ce Shekau dai ya mutu sau da dama, tun bayan da ya karbi ragamar kungiyar Boko Hara a 2009. Da farko an ce ya mutu a wani fada, a wani lokaci sojoji an ce sojoji sun ce sun halaka shi, amma daga baya sai ya sake bayyana. Sai dai a wannan karon ra'ayin masana ya dace da cewa Shekau ya mutu. Gamsassun bayanai hadi da wani sauti na muryar shugaban kungiyar ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi sun tabbatar cewa Shekau ya kashe kansa lokacin da mayakan reshen kungiyar IS a yammacin Afirka wato ISWAP, suka yi masa kawanya suka nema ya mika wuya. Haka bayanan hukumar leken asirin Najeriyar ma sun tabbatar da labarin, ko da yake rundunar sojan kasar da a baya ta sha bayar da labarin mutuwarsa, yanzu tana taka-tsan-tsan. Mutuwarsa za ta sa Boko Haram ta kara yin rauni a hannu guda kuma ISWAP za ta kara yin karfi, domin wasu daga cikin 'ya'yan Boko Haram za su yi mata mubaya'a.

Nigerien Boko Harams Führer Abubakar Shekau
Ta tabbata jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya kashe kansaHoto: picture-alliance/AP Photo
Mali Frankreich beendet die Operation „Barkhane“
Sojojin rundunar Barkhane ta Faransa, sun fice daga MaliHoto: AP Photo/picture alliance

Faransa ta gaza a yankin Sahel a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, tana mai cewa da alama har yanzu sojojin kasashen ketare sun kasa inganta lamuran tsaro. Ta ce bayan harin ta'addanci mafi muni tun bayan samun 'yancin kan kasar Burkina Faso, ministan harkokin wajen Faransa Yves Le Drian a wannan mako, na kai wata ziyara a kasar domin mika jajen kasarsa. Ko da yake makasudin ziyarar shi ne, tattauna batutuwa na tsaro da shugaban kasar Burkina Fason. Harin ta'addancin da ya yi sanadi na mutuwar akalla mutane 160, ya auku ne a garin Solhan kusa da barikin soji na Sebba. Sai dai sojoji ba su kai wa al'ummomin yankin dauki ba. Burin girke sojojin Faransa a yankin kan iyakar kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, shi ne bai wa sojojin kasashen uku horo kan yadda za su dakile ayyukan 'yan ta'adda. Tun a farkon shekarar 2020 sojoji 2000 na rundunar Barkhane ke a yankin, amma haka bai kawo ingantuwar lamuran tsaro ba. Sai dai Faransa na dora laifin a kan raunin sojojin kasashen na Afirka.