1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ukraine na kara ta'azzara

August 28, 2014

Mahukuntan kasar Ukraine sun tabbatar da cewa dakarun kasar Rasha da'yan Awaren gabashin kasar, sun kutsa kai yankin kudancin Ukraine din.

https://p.dw.com/p/1D3NJ
Hoto: picture alliance/AP Photo

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce ya damu matuka da rahotannin da ke nuni da cewa rikicin Ukraine na bazuwa zuwa yankin kudancin kasar inda ya ce in har hakan ya tabbata to tabbas zai haifar da gagarumin tashin hankali a kasar. Ban ya bayyana hakan ne ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric yana mai cewa ba zai yiwu al'ummomin kasa da kasa su zuba idanu suna kallon ci gaban wannan tashin hankali da rikici da ya ke kara kamari a yankin a gabashin Ukraine da kuma ke barazanar bazuwa zuwa yankin kudancin kasar ba. Tuni dai Amirka da kawayenta suka fara nuna tasu damuwar inda suke duba yiwuwar sake kakabawa Rasha takunkumi. A hannu guda kuma kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar na gudanar da wani taro kan batun rikicin na Ukraine.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane