1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ukraine na zafafa

May 5, 2014

Daruruwan masu goyon bayan ci gaba da kasancewa a Ukraine sun yi maci a garin Odessa na gabashin kasar, bayan kisan karshen mako yayin arangama da 'yan Aware.

https://p.dw.com/p/1Btxn
Hoto: Reuters

Lamuran gabashin kasar ta Ukraine na kara tabarbarewa. Cikin karshen mako Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna ta wayar tarho da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan sakin 'yan kungiyar tsaro da hadin kai Turai da ka yi daga yankin na gabashin Ukraine.

'Yan aware masu goyon Rasha sun farma ofishin 'yan sanda suka suka kwato fiye da mutane 60 da aka tsare masu goyon bayan rasha. A karshen mako gwamnati ta dauki mataki tsare wadanda ake zargi da neman tayar da zaune tsaye. Kusan mutane 10 sun hallaka yayin ayyukan soji tsakanin garuruwan Kramatorsk da Slavyansk. Mafiya yawan mutanen yankin na bukatar zaman lafiya domin tafiyar da rayuwa ta yau da kullum kamar yadda aka saba, kamar yadda wannan mazaunin garin na Kramatorsk ke cewa:

"Abin da muke bukata shi ne rayuwa cikin nutsuwa, wannan kawai muke so. Ba ma bukatar wani abu bayan haka, nutsuwa da zaman lafiya, dukkaninmu 'yan Ukraine ne, 'yan uwan juna muke. Mun dade muna rayuwa tare da juna. Babu mai bukatar yaki. Abin da mutum yake bukata shi ne zaman lafiya, ga kowa ba yaduwar makamai."

Rikicin da ke faruwa cikin yankin gabashin kasar ta Ukraine na ci gaba da daukan hankali musamman manyan kasashen duniya da ke fafutukar ganin an samu zaman lafiya. Amma ga dukkan alamu da sauran aiki domin ranar Jumma'a da ta gabata kimanin mutane 46 sun mutu, lokacin da masu goyon bayan Ukraine suka hurga wuta cikin wani gini da 'yan aware masu goyon bayan rasha suka shiga, yayin wata arangama.

Ostukraine Krise Checkpoint bei Slowjansk 04.05.2014
Hoto: Vasily Maximov/AFP/Getty Images

Mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha, Grigori Karasin, ya ce abubuwan da suke faruwa na nuni da dace mahukuntan Ukraine sun kasa, kuma suna neman dauki:

"Abin bakin cikin da ya faru a garin Odessa ranar 2 ga wannan wata na Mayu, ya nuna irin rikicin siyasar kasar da sukurkucewar lamura ga Ukraine. Makonni biyu bayan amince da yarjejeniyar Geneva kan magance zaman tankiya. Yanzu tambayar ita ce mai aka cimma trun lokacin? Mahukuntan Ukraine ya dace su dauki mataki gyara lamura cikin yankin kudu maso gabashin kasar, kamar yadda aka tsara karkashin yarjejeniyar birnin Geneva. Ga dukkan alamu suna bukatar tallafi daga kasashen ketere kan tattaunawar. Ina tsammani Mahukuntan Kiev bukatar masu shiga tsakani kan halin da ake ciki a kudu maso gabashin kasar."

Ukraine Luhansk Checkpoint prorussische Aktivisten 4.5.14
Hoto: Reuters

Yanzu dai ministan harkokin cikin gida na Ukraine Arsen Avakov ya ce za a sauya wuraren da ake tsere da sauran 'yan awaren da aka kama 42, domin kare kubutar da su. Maganar da ake bankuna sun rufe cikin manyan garuruwan gabashin kasar, sakamakon bazuwar tashin hankali da raguwar miyagun laifuka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal