1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Sabon rikicin 'yan gudun hijira

March 4, 2020

Rundunar hadin gwiwa ta Frontex da ke kula da tsaron kan iyakokin kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU, za ta tallafawa kasar Girka dangane da matsalar kwararar 'yan gudun hijira daga Turkiyya.

https://p.dw.com/p/3YrDH
Migranten an der griechisch-türkischen Grenze
'Yan gudun hijira na neman hanyoyin shiga kasashen TuraiHoto: picture-alliance/dpa/Xinhua/D. Tosidis

Rundunar ta Frontex dai za ta tallafawa jami'an kula da kan iyakar kasar Girkan da motoci da jirage masu saukar ungulu da ma kayan aiki domin kare kan iyaka da nufin dakile yunkurin 'yan gudun hijirar da Turkiyya ta saki shiga kasashe mambobin kungiyar ta EU. Tun dai a shekara ta 2015 ne yayin da nahiyar Turan ta samu kanta tsundum cikin matsalar kwararar 'yan gudun hijirar biyo bayan bude kan iyaka da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi, aka kafa rundunar tsaron ta Frontex, da nufin bayar da tsaro a kan iyakokin kasashen na EU a yayin da al'amura suka rincabe. Kasar Girka dai ta bukaci taimakon rundunar ta Frontex ne bayan da Turkiyya ta budewa 'yan gudun hijirar kofa tare da ba su damar kama gabansu, duk kuwa da yarjejeniyar da suka cimma da kungiyar Tarayyar Turan EU dangane da tsare 'yan gudun hijirar a kasarta domin kar su kwarara zuwa nahiyar Turan.#b#

Bukatar azgazawa 'yan gudun hijira

Fabrice Leggeri shi ne babban kwamandan wannan runuduna ta Frontex ya kuma ce duk da suna son yin aiki da dokokin kan iyakokin kasashen Turai na Schengen, wato shiga kasashen da ke karkashin wannan doka ba tare da shinge ba, ya kuma zama wajibi su yi nazarin kare kan iyakokinsu daga kasashen da ba sa cikin tsarin na Schengen. Sai dai fa wannan rundunar hannayenta a daure suke, domin bisa kundin tsarin kafa ta, ya jami'an na Frontex ba su da damar daukar kowanne irin mataki na kai tsaye ba, sai dai su yi aiki kan tsarin tsaron kasar da ta nemi su kai mata dauki. A kwai bukatar kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa a nasu bangaren, su yi aikin hadin gwiwa domin tallafawa 'yan gudun hijirar da ke cikin halin tsaka mai wuya.