1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Zimbabuwe ya mamaye jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala
November 17, 2017

Rikicin Zimbabuwe ya mamaye jaridun Jamus, yayin da sojoji da suka karbe iko da mulkin kasar ke kokarin neman mafita ga dorewar dimokradiyyar kasar ta kudancin Afirka.

https://p.dw.com/p/2nqHO
Simbabwe Robert Mugabe hält Rede an der Uni
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/T. Mukwazhi

A wannan makon ma dai sharhin Jaridun Jamus ya maida hankali ne akan dabarwar siyasar kasar Zimbabuwe

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa sharhinta mai taken “Bata sauya zani ba" dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a Zimbabwe 

Jaridar ta ce a ranar Litinin din da ta gabata wani abu da ba a taba tsammani ba ya wakana, inda aka wayi gari sojoji suka karbe iko a Zimbabwe. Kimanin kaso uku cikin kaso hudu na al’ummar kasar basu san wani mulki ba sai na Mugabe. Mulkin nasa ya kasance tamkar na mutu ka raba. Kakakin rundunar sojojin kasar ya nunar da cewa a karshe al’ummar kasar sun tsira daga Mugabe abu mafi muhimmanci kuma sun tsira daga matarsa. Mugabe dai ya sanar da cewa zai tsaya takara a zabe na gaba, wanda ake ganin zai nada matarsa Grace Mugabe mai shekaru 53 a duniya a matsayin mataimakiyarsa, kafin daga bisani ya ba ta shugabancin kasar. 

Simbabwe PK Armee - General Constantino Chiwenga
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Ana dai iya yaba wa sojojin da suka kwace mulkin, sai dai kuma idan aka yi la’akari da zargin da ake cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa na da hannu a juyin mulkin, ana iya cewa ba ta sauya zani ba. Akwai dai fata na yi wuwar sojojin su shirya sahihin zaben da ke tafe a shekara mai zuwa kana idan ‘yan adawa suka hada kansu, ‘yan kasar na iya zaben shugaban da ya dace bayan tsahon shekaru 37 na mulkin Mugabe.
Ita kuwa jaridar “die tageszeitung“ a sharhinta mai taken "An sallami macen da ta fi kowa arziki a Afirka" Jaridar ta rubuta sharhin nata ne kan korar da sabon shugaban kasar Angola João Lourenço ya yi wa Isabel dos Santos da takasance shugabar kamfanin man fetur na kasar daga kan mukaminta wadda kuma ta kasance 'ya ga tsohon shugaban kasar José Eduardo dos Santos da ya shugabanci kasar daga shekara ta 1979 zuwa shekara 2017. Lourenço wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Angola cikin watan Agustan da ya gabata ya banbanta kansa daga wanda ya gada sakamkon bijiro da sababbin tsare-tsare da sauye-sauye a kasar wanda ya sanya da dama daga cikin jiga-jigan 'yan siyasar kasar rasa mukamansu.

Angola Isabel dos Santos spricht zu Journalisten
Hoto: Reuters/E. Cropley

Angola dai ita ce ta biyu a kasashen Afirka da ke da arzikin man fetur bayan Najeriya, sai dai cikin shekaru ukun da suka gbata, kasar ta tsinci kanata cikin matsin tattalin arziki sakamakon faduwar farashin danyan mai a duniya. Korar Isabel dai ka iya janyo nakasu ga jam'iyyar adawa a makwabciyar kasar Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Kwango. Mijinta Sindika Dokolo hamshakin dan kasuwa ne a Kwango, wanda kuma ke kan gaba wajen sukar gwamnatin Shugaba Joseph Kabila da kuma ba da goyon bayansa ga jam'iyyar adawa, kuma yana yin hakan ne da taimakon gwamnatin Angola, wanda za a iya cewa ba abu ne mai yi wu wa ba nan gaba.