1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kabore na kan gaba a zaben Burkina Faso

Yusuf BalaNovember 30, 2015

A sakamakon da ke fitowa a ranar Litinin din nan kimanin kashi 41 cikin dari na kuri'un da aka kada sun kasance na Mista Kabore.

https://p.dw.com/p/1HEyu
Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Roch Marc Christian Kabore
Roch Marc Christian Kabore lokacin da yake kada kuri'aHoto: DW/K. Gänsler

Tsohon Firayim Minista a kasar Burkina Faso Roc Marc Kabore na zama kan gaba da rinjayen kuri'u a sakamakon farko da ya fara fita a zaben kasar da ke zama mai tarihi bayan gwamnatin Blaise Compaore da zanga-zangar al'ummar Burkina Faso a watan Oktoba na 2014 ta yi awon gaba da mulkinsa. Wannan zabe dai na zama mai muhimmanci ga wannan kasa ta Burkina Faso mai albarkatun zinare da auduga.

A sakamakon da ke fitowa a ranar Litinin din nan kimanin kashi 41 cikin dari na kuri'un da aka kada sun kasance na Mista Kabore yayin da Zephirin Diabre tsohon ministan kudi a kasar ke da kashi 29 cikin dari a cewar hukumar zaben kasar mai zaman kanta.

Yadda aka yi zabe lami lafiya a kasar ta Burkina Faso wata alama ce da ke nuna irin ci gaban da kasar ta samu a fannin dimokradiya da kuma ke zama abin koyi ga sauran kasashen Afirka musamman masu neman dawwama akan mulki ga misali Burundi da Jamhuriyar Kwango inda aka yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulki dan tazarce.