1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruɗani kan sayar da kamfanin lantarkin Najeriya

October 30, 2012

Hukumar da ke kula da sayar da kadarorin gwamatin Najeriya da hannun jarin da gwamantin ke da shi a wasu kamfanonin kasar ta ce ta amince da sayar da wasu kamfanonin wutar lantarkin kasar goma sha biyar.

https://p.dw.com/p/16ZjU
Hoto: picture-alliance/dpa

Cefanar da kamfanonin samar da wutar lanatarkin na Najeriya dai ga 'yan kasuwa ya jawo kace-nace a ƙasar musamman ma dai daga masana tattalin arziki da kuma talakawan ƙasar inda ake zargin masu uwa a gindain murhu da ƙoƙarin wa-ka-ci-ka- tashi da dukiyar a tsarin.

Gwamantin tarrayar ta Najeriya dai ta yi kunnen uwar shegu game da wannan batu inda ma ta fito fili ta ce ta amince da ɗaukacin cinikin kamfanonin na samar da wutar lantarkin da a baya su ke ƙarƙashinta.

Shirin da ke zaman irin sa na farko ga kasar da ta kashe sama da dallar Amurka miliyan dubu arba'in amma ta kai ga kasa samar da mega watta dubu huɗu na wuta dai ya zauna ya kalli komawar ɗaukacin masana'antar ya zuwa hannun wasu 'yan ƙalilan ɗin 'yan kasar da su ka daɗe su na taka rawa a cikin harkokin siyasar ƙasar amma kuma ba'a san su da ƙwarewa ga batun na samar da makamashin na wutar lantarki ba.

Majalisar saida kadarorin gwamnati ta ce shirin wani cigaba ne

An dai kai ruwa rana a tsakanin gwamnonin jihohin kudu maso kudancin ƙasar da su ka cesu na adawa da yadda aka kai ga cinikin ɗaya daga cikin kamfanonin, to sai dai kuma majalisar sayar da kaddarorin ƙasar ta ce babu gudu babu jada baya ga shirin da ke zaman irin sa na farko a daukacin nahiyar Afrika da kuma a cewar Aterdo Peterside da ke zaman shugaban kwamitin ƙwarraru na hukumar kula da sayar da hannun jarin ƙasar babban ci gaba ne.

Nigeria Solar-Lampen in Katsina
Lantarki daga hasken ranaHoto: DW

'Wannan ne ƙoƙari na farko ga wata ƙasar Afrika na cefanar da harkokin wuta. An yi a wani bangare na Asiya da wani bangare na Turai, amma ba a taɓa ba a Afrika. Saida kamfanonin babban ci gaba ne. Abun da na ke son ince shine dole ne kabi kaidojin ciniki. In kuma tayin haka wani zai matsa maka lamba ba haufi. Ina jin babu wata gwamanati ko wani minister da ba ya fuskanatar matsin lamba. Amma kuma a kotu ba hujja bane ka ce an matsa maka lamba in ba ka yi ba daidai ba. Abun da ya ke shi ne ka yi abu mai ma'ana a koyaushe.'

Saida kamfanonin zai sanya Najeriya samun ɗumbin kuɗaɗe

Nigeria dai ta ce ta na saran samun a kalla naira miliyan dubu ɗari huɗu daga saida kaso sittin cikin ɗari na hannun jarin kaddarorin na wuta, adadin kuma da bai wuci kaso goma cikin dari na yawan kuɗin da tarrayar ta Najeriyar ta kashe domin inganta su ba, abun kuma da ke ci gaba da janyo ɗaga hakarkari da jijiyar wuya a Najeriyar da a baya ta sayar da kaddarorin cikin araha amma kuma ta gaza samun ingantar tafi da su a hannun 'yan kasuwar da ke zaman sabbabin mamallakan su.

Duk da cewar dai su na taƙama da gaiyato ƙwarraru domin tafi da harkokin su, babu dai koda kamfanin cikin gida gudan da yai nasarar sayen hannun jarin da ke da ƙwarewa ga batun tafi da al'amuran wutar ƙasar ta Najeriya, to sai dai kuma a cewar shugaban kwamitin na kwarraru zancen banza ne ga masu zargin son zuciya dama son kai a cikin cinikin.

Nigeria Strom Elektrizität Energie Generator Lagos
Yawan amfani da injin samar da wutaHoto: picture-alliance/dpa

'Shin akwai wanda zai bani shaidar da ke tabbatar da waɗanan zarge-zarge? In akwai dan Allah a bamu. Abu ne mai sauki ga wani ya tashi ya yi ƙazafin cin hanci ko rashawa da sauransu. Amma in akwai mai shaida to dan Allah muna jira.'

A cikin watan Satumban da ya gabata ne dai aka kai ga sallamar da ministan makamashin wutar Nijeriyar da aka zarga da ƙoƙarin cefanarwa da kansa wasu daga cikin kamfanonin samarwa da kuma rabon wutar to sai dai kuma har yanzu ana danganta wasu kamfanonin da wasu daga cikin manyan mazauna fadar gwamantin kasar ta Aso rock.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar