1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani a kan lamuran tsaro a Najeriya

Ubale MusaDecember 8, 2014

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da ranar bikin tunawa da tsofaffin sojoji, a dai-dai lokacin da sababbin ke kokarin shawo kan bacin sunan da ya kaisu ga yin dare cikin yakin da suke da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1E0yg
Hoto: picture alliance/AP Photo/Gambrell

A gefe daya dai ana biki ana cashewa da nufin tuna 'yan mazan jiyan da suka kai ga jawo kima da martaba a yake-yaken da dama ga Tarayyar Najeriyar da ke tsakiyar wani yakin yanzu. A wani bikin tunawa da ranar tsofaffin sojojin da suka sadaukar da rayukansu ciki da ma wajen kasar da nufin tabbatar da duniya tai kyau. To sai dai kuma a daya bangaren magadansu da har yanzu ke cikin gidan sojan kasar ta Najeriya ne dai ke neman jawo kunya ga kasar da ake yiwa kallon giwa a nahiyar Afirka ta fannin sojan, amma kuma masu dinkin hula ke neman gagarar sarrafa ta da sunan yaki da ta'adda.

Mafarauta da fulani ne ke yakar ta'addancin

Kama daga Mubi ya zuwa Gombi dama Hong dai mafarauta da Fulani ne suka ciri tuta a cikin yakin da ke cikin shekararsa ta biyar, da kuma ya bata rai cikin gida da ma wajen kasar. Bikin na yau da kuma kila ke zaman na karshe ga gwamnatin da ta share shekaru hudun farko tana fadin ta kusa kai karshe a cikin yakin, amma kuma har yanzu 'yan kasar ke kallon ta da nisa, ko a farkon mako dai akalla 'yan mata 20 ne kungiyar Boko Haram ta kai ga sake sacewa a Najeriyar.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/AP

Shi kansa shugaban kasar da ya sha fada yana sauyawa a kan ikirarin nasarar da sojojin ke samu a cikin yakin dai, daga dukkan alamu ya kai karshe ga kodawa sojojin kai, da bai bawa muhimmancin da suke fatan gani cikin jawabinsa ga 'yan bikin ba.

“A yayin da ake bikin ranar tunawa da tsofaffin sojojin ranar 15 ga watan Janairu na ko wacce shekara da ke zaman karshen ranar yakin basasar kasarmu, muna yaba kwazo da juriya ta sojojinmu wajen tunkarar yaki da ta'addancin da ke cikin wasu sassan kasarmu, sun nuna matukar imaninsu ga Tarayyar Najeriya”.

Rawar da sojojin Najeriya ke takawa ta sauya

Tuni dai masana tarihin sojan kasar a can baya ke mamakin sauyin rawa da ma tabacin da ta dauki sojan daga na gwamna shanun gwamna ta nemi maida su Magen Lami da bata cizo ba kuma yakushi duk da man da take faman sha ga kasar. To sai dai a tunanin Kanal Micah Gaiyya da ke zaman shugaban kungiyar tsofaffin sojojin kasar wai sauyin yafi kama da zamani, maimakon gazawar da 'yan kasar ke gani a halin yanzu.

“Yaki na jiya mun sani a kan ja layi ga abokan gaba amma yanzu babu. A cikin mu akwai 'yan adawa, ina jin shine ban-bancin, amma dai horarwar iri daya ce. Ban san cewar mafarauta sun kori Boko Haram in da soja ya kasa ba, kuma kasan zamani na sauyawa, ba a Najeriya kadai ba. Abin da muka yi da, yaran yanzu ba zasu iya ba kuma ba laifinsu bane”.

Hare-haren ta'addanci a Najeriya
Hare-haren ta'addanci a NajeriyaHoto: Reuters

An dai rika ta'allaka tsohon gwamnan jihar Borno kuma jigo a cikin jam'iyyar PDP Ali Modu Shariff da hannu ga batun jirgin da aka kama a jihar Kano makare da makamai a kan hanyarsa ta zuwa Chadi, to sai dai kuma a fadar kakaki na Shariff din Inuwa Bwala kokarin danganta mai gidan nasa da jirgin da aka ce ya kai ga ziyara har gindinsa dai, yafi kama da kokari na siyasar bata masa suna. Abun jira a gani dai na zaman dangatakar da ke tsakanin yakin ta'addancin kasar da kuma siyasar da ke dada muni yanzu.