1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudanin siyasa a Spain game da Kataloniya

Abdullahi Tanko Bala
October 30, 2017

A yau litinin Spain ta shiga sabon wadi na dambarwar rikicin da ya dabaibaye kasar game da ayyana ballewar Kataloniya da majalisar dokokin yankin ya yi.

https://p.dw.com/p/2mipC
Spanien - Demonstrationen für die Einheit von Spanien und Katalonien in Barcelona
Hoto: Getty Images/AFP/P.-P. Marcou

A yau litinin Spain ta shiga sabon wadi na dambarwar rikicin da ya dabaibaye kasar game da ayyana ballewar Kataloniya da majalisar dokokin yankin ya yi.

Shugabannin Kataloniyan wadanda gwamnatin Spain ta sallama sun yi kiran nuna turjiya ta hanyoyi na dimokradiyya, lamarin da ke sanya fargaba a nahiyar Turai cewa rikicin na Spain na iya daukar tsawon lokaci da ma watakila kara yin muni.

Babu dai tabbas ko za a tuhumi tsohon shugaban yankin na Kataloniya Carles Puigdemont da laifin cin amanar kasa sakamakon ayyana ballewar da yankin ya yi daga kasar kasar Spain.

A jiya Lahadi dubban jama'a sun gudanar da zanga zanga a Madrid domin adawa da ballewar yankin Kataloniyan daga Spain.