1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rukunin farko na dakarun AU sun sauka a Somalia

March 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuQv

Rukunin farko, na sojojin ƙungiyar taraya Afrika, ya isa a Somalia, da zumar kwantar da tarzomar da ke ci gaba da ɓarkewa a wanan ƙasa.

Wananayari na sojoji 30 yankasar Uganda ya sauka da sahiyar yau a birnin Baidoa .

A jimilce sojoji dubu 8 ne AU ta kudurci aikawa a kasar Somalia, to saidai ta na fuskantar matsaloli, ta fannin tattara wannan dakaru da kuma samar masu issasun kayan aiki.

Ya zuwa yanzu,ƙasashen Uganda, Nigeria, Burundi, Ghana da, Malawi, sun alkawarta bada sojoji kimanin dubu 4.

Saidai a nasu gefe, dakarun kotunan Islama sun yi kashedi ga rundunar AU, da cewar, mudun ta sa ƙafa a Somalia, to zata gamuwa da ajalinta.

A wani jawabi da ya gabatar yau, a majalisar dokoki, shugaban ƙasar Somalia, Abdulahi Yusuf Ahmed, ya bayyana 16 ga watan Aprul mai kamawa, a matsayin ranar da za buɗa taron haɗin kai, inda a tsawan watani 2, al´ummomin Somalia,za su gayawa juna gaskiya,ƙeƙe- da ƙeƙe, su kuma yafewa juna.